2019: ‘Yan Najeriya a kasar Britaniya sun yi zanga-zangar kin amincewa da Buhari ya zarce

0

‘Yan Najeriya mazauna kasar Britaniya sun gudanar da zanga-zanga a gidan Najeriya da ake Kira gidan Abuja dake birnin Landan domin nuna rashin goyan bayan furucin da Buhari yayi na fitowa don sake tsayawa takarar Shugabancin Najeriya a karo ta biyu.

Idan ba a manta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana wa ‘yan Najeriya aniyar sa ta sake tsaya wa takarar Shugabancin Najeriya a karo ta biyu a taron jiga-jigan jam’iyyar sa ta APC a Abuja.

Shugaba Buhari dai ya tafi kasar Britaniya domin yin hutu sannan da shirin halartar taron Kungiyar kasashen rainon Ingila da za a yi a ranakun 16-17 a kasar na Britaniya.

A maida martani da fadar Shugaban kasa tayi game da wannan zanga-zanga, ta bayyana cewa shiri ne na ‘yan adawa don aci wa Shugaban Buharu mutunci da Najeriya.

” Wannan shiri ne na makiya Shugaban Kasa musamman ganin cewa gwamnati ta maida hankali wajen bankado wadanda suka wawushe kudin kasar sannan ta tilasta musu da su dawo da su. Shine suka shirya irin wannan abin kunya domin su kunya ta shugaba Buhari.

” Muna Kira ga abokanan huldan kasuwancin mu da ‘yan kasar waje da Kada su ko Kula wannan zanga-zanga da akayi. Shiri ce kawai na wadanda ke da guntun Kashi a bayan su don SU gurgunta kyawawan ayyukan da wannan gwamnati ta somo tun bayan gawan ta Kan karagar mulki.

Share.

game da Author