2019: Yadda Buhari ya rufe bakin ’yan tsugudidin da ke rabe a jikin sa

0

Masu lura da al’amurran siyasa kama daga na cikin gwamnatin APC, masu adawa da kuma ‘yan ba ruwan mu, sun bayyana ra’ayoyi da dama dangane da yadda Shugaban Kasa ya fito tun ana saura shekara daya cur a yi zabe ya ayyana bukatar sa ta neman APC ta sahale masa ya sake tsaywa takara karo na biyu a zaben 2019.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta yi wani tsinkayen da a bisa dukkan alamu, furucin wanda Buhari yayi, alama ce ta kashe kaifin bakin duk wasu masu kullen siyasa a lokacin da shi shugaban kasa din ba ya kasar.

Idan aka yi duba, za a fahimci cewa Buhari ya yi wannan bayani ne a ranar da zai tashi daga Abuja zuwa birnin Landan, domin halarata taro, wanda za a gudanar bayan isar Buhari kasar Ingila sa sati daya.

Bayan kammala taron kuma ana sa ran shugaban kasar zai tsaya ya kara kwanaki domin ya kara ganin likitan sa.
Tambaya a nan ita ce, me ya sa ba zato ba tsammani Buhari ya bayyana aniyar sa ta sake tsayawa takara sa’o’i kadan kafin ficewar sa daga kasar nan?

Idan ba a manta ba, a lokacin da Buhari ya yi doguwar jinya a Landan, ta baya-bayan nan wadda ya awo bayan ya shafe watanni a can, an yi ta rika yada ji-ta-ji-ta cewa da wuya ya dawo da ran sa. Ko kuma idan ma ya dawo din, to zai hakura ne da mulki, ya sauka ya bai wa wani.

Rahotanni da dama sun bayyana ce a wannan lokacin, wasu gaggan ‘yan APC sun rika kai gwauro su na kai mari sun a shiga daki su kulle kan su inda suke kulle-kullen wanda zai zama mataimakin shugaban kasa idan ta Allah ta kasance kan Buhari, kamar yadda aka rika yayata cewa ai ya mutu.

Shi kan sa Buhari, bayan ya dawo, ya tabbatar da an yi wannan kulle-kullen domin a cikin jama’a ya taba bayyana cewa ya na sane da kulle-kullen da wasu ‘yan APC sua rika yi.

An rika zargin wani gwamnan Arewa a cikin wannan kulle-kulle, duk da dai bai fito ya furta ba.

Wasu da dama sun rika zargin Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai. Zargin ya kara fitowa fili ganin yadda Gwamnan bai je tarbar Buhari a filin jirgin sama na Kaduna ba, sai dai mataimakin sa ya wakilce shi.

Da alama hannun ka mai sanda ne Sanata Shehu Sani ke yi wa El-Rufai, a lokacin da a shafin sa na soshiyal midiya ya bayyana cewa bayyana son sake tsayawa takara da Buhari ya yi, to daidai ne, domin kashe bakin tsanya, kuma ya rufe bakin magulmata da ‘yan tsugudidin neman hawan mulki ta bin wasu hanyoyi na ‘yan dabaru.

Sai dai kuma wani abin la’akari a nan shi ne El-Rufai ne mutum na farko da ya fara bayyanawa a shafin sa na facebook cewa su na murna Buhari zai sake tsayawa takara.

Shi kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ahmed Makarfi, cewa ya yi ai fitowar Buhari baa bin mamaki ba ne, rashin fitowar sa it ace abin magana.

Ya ce PDP dama tuni ta ke zaman jiran dakon fitowar Buhari, wanda y ace zai sha kaye tun ma kafin a kai ga kammala zabe.

Share.

game da Author