2019: Shammatar mu Buhari ya yi a 2015, muka kai shi can kololuwa, ashe-ashe – Dan takarar shugaban kasa

0

Wani masoyin Buhari, da aka yi gwagwarmayar yakin neman zaben shugaban kasa da shi a karkashin jam’iyyar APC, mai su Femi Olufumilade, ya bai wa jama’a mamaki, ganin yadda ya dawo daga rakiyar tafarkin Buhariyya, a yanzu kuma ya fito ya na neman kujerar shugaban kasa a karkashin SDP.

A wata ziyara da ya kawo a hedikwatar ofishin PREMIUM TIMES a Abuja, an yi wata doguwar tattaunawa da shi, inda ya bayyana dalilin sa da dawowa daga rakiyar Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin ta.

Ya ce wato ya tsaya ya yi tunani ne cewa a 2015 sun kai Buhari a matsayin da kwata-kwata bai kai ba. Sun yi tunanin ya iya sallah, amma ashe ko alwala ma bai iya ba.

Ya ci gaba da cewa a tunanin su Buhari zai ba marada kunya, ganin yadda ya nace sai ya yi mulkin Najeriya, har karo hudu, amma ashe abin ba haka ya ke ba.

“Da farko dai idan shi Buhari zai yi magana, zai ce maka abubuwa uku ya ce zai fi maida hankali a kai. To sai mu duba mu gani. Zai ce maka batun rashin tsaro ai ya gama da Boko Haram. To tabbas ya yi kokari amma da sauran rina a kaba, amma ba a gama da su ba kamar yadda ake ikirari.

“Inda ya bata rawar sa da tsalle, shi ne yadda ya bari rikicin Fulani makiyaya da manoma ya yi muni kwarai. An dade ana rikicin nan bayan hawan mulkin sa ya yi kamari sosai. Amma sai ya kauda kai, tamkar abin bai dame shi ba.

Ya kuma yi nuni da yawn kashe-kashe da garkuwa da jama’a da ke ta kara ta’azzara sosai a kasar nan.

“Wani haushin kuma shi ne, yadda daga baya ya maida hankali kan rikicin, duk mai hankali zai ga kamar sai da aka tirsasa shi ma ba da son ran sa ya amaida hankali kan rikicin ba.”

Yayin da ya ke cewa shi ya tabbatar idan ya zama shugaban kasa sai ya fi kyautata wa ‘yan Najeriya, fiye da irin takun Buhari, Olufimilade ya ci gaba da cewa batun cin hanci da rashawa tabbas Buhari ya yi kokari ganin irin labaran da ake ji na kudaden da ake fallasawa.

Sai dai kuma inda gizo ke saka a ta bakin Olu, shi ne Buhari kwata-kwata bai san abin da ke faruwa a cikin gwamnatin sa ba. Don haka, sai ya zama tamkar mutumin da ya jibga riguna 9 a jikin sa, amma gadon bayan sa a waje.

Ya ce sai bayan Buhari ya sauka zai yi mamakin irin yadda shi ma za a rika fallasa harkalla da barankyankyamar da ake tafkawa a gwamnatin sa. Don haka ya ce Buhari ya yi hattara, makusantan sa za su kai gwamnatin sa su baro, amma ba zai gane ba, sai ya sauka daga mulki.

An tambaye shi batun inganta tattalin arziki, sai ya ce to ai wannan kowa ma shaida ne. Idan an samu saukin rayuwa kan gwamnatin da ta shude, mutane su ne shaida. Idan farashin kaya ya yi kasa ko kuma tashi ya yi bayan Buhari ya hau mulki, to jama’a duk sun sani.

Share.

game da Author