2019: Ku yi shirin korar Buhari ko ta halin kaka – Hudubar Obasanjo

0

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga Gamayyar Kungiyar Hadin Kan Ci Gaban Najeriya, Coalition for Nageria Movement da su yi shirin fafata yakin kwace mulki daga hannun Buhari.

Obasanjo ya ce yakin farko shi ne mallakar katin rajista yin zabe. Ya yi wannan bayani ne a da wurin kaddamar da kungiyar reshen jihar Oyo.

A wuri kaddamarwar a garin Ibadan, ya na mai kara yin kira da cewa su sani fa nan gaba za su fuskanci barazana, saboda matsayin da suka dauka na jajircewa ceto Najeriya.

Ya ce kowa zai yi tananin kamar ba abu ne mai yiwuwa ba, amma da karfin Allah da addu’a da kuma jajircewa, hakar su za ta cimma ruwa.

Daga nan sai ya kara maimaita musu cewa su dauki batun katin jefa kuri’a da gaske.

Obasanjo ya kafa wannan kungiya ce bayan ya rubuta wa Buhari budaddiyar wasika inda ya nemi ya hakura haka nan, bai cancanci sake tsayawa takarar zabe a 2018 ba.

Obansanjo dai ya ce a matsayin sa bai kamata ya ji tsoron gaya wa kowa gaskiya ba, kuma bai kamata wani yi wa Najeriya tukin-ganganci ba shi kuma ya zuba masa ido ya na kallon sa.

Share.

game da Author