2019: Idan Buhari ya zarce shikenan sai kuma gawar’yan Najeriya – Inji gwamna Fayose

0

Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose, ya bayyana cewa za su yi kamfen domin tabbatar da cewa ‘yan Najeriya basu sake yin kuskuren zaben Buhari a karo na biyu ba. Ya na mai cewa idan har aka kuskura aka sake zaben sa a karo na biyu, to Buhari kashe Najeriya zai yi.

Fayose ya ce Buhari ya kasa fahimtar cewa tsufa ya cim masa, ya kamata ya ja gefe. Amma tunda ya kafe ya ce sai ya ci gaba da mulki, to Fayose ya ce, ga fili nan, 2019 na tafe, za a maida shi Daura ko Kaduna.

Gwamna Fayose ya ce banda tsufa da ya cimma Buhari har ba ya iya wani kuzari a mulki, ya kuma baras da damar da ‘yan Najeriya su ka ba shi. Domin dai ko kadan bai yi abin da wadanda suka zabe shi su ka yi tunanin zai yi ba.

“Ai batun sake mulkin sa ma bai taso ba. Ba za mu bar dattijo tsarar kakan mu ya sake mulkin mu ba kuma.” Inji Fayose.

Ya ci gaba da cewa Buhari bai cancanci zango na biyu ba. “Kamata ya yi kada ‘yan Najeriya su raka asara da guda. Ya kamata idan zaben 2019 ya zo, to a yi masa ‘Allah raka taki gona.’

‘Illar da mulkin Buhari ya yi wa kasar nan ta fi alherin da ya shuka. Idan zabe ya zo kowa ya fito ya yi masa Allah-raka-taki-gona, a kore shi daga kan mulki da karfin kuri’u. Domin yadda ya dagula kasar nan, hakan na nuni da cewa zai yi matukar saukin kayarwa a ranar zaben Shugaban Kasa.

“A dukkan alkawurran da ya dauka babu inda ya yi wani abin kwarai. Yaki da cin hanci bulkara kawai ya keyi. Tattalin arziki kuwa ai talaka shi ya san irin wahalar da ya ke sha. A fannin tsaro kuma ku na dai ji da ganin yadda ake ta karkashe mutane a jihohi da dama.

“Fitowar da Buhari ya yi ya ce zai sake tsayawa takara, ai raina wa ‘yan Najeriya wayau ne kawai ya yi. Kamata ya yi ya tafi gida kawai ya kwant ya huta.” Inji Fayose.

Share.

game da Author