ZUWAN BUHARI FILATO: Duk da dubban jami’an tsaro, an kai hari wani kauye

0

Duk da dubban jami’an tsaro da aka tura Jihar Filato don samar da tsaro an sami wasu mahara da suka kai hari kauyen Nzharuvo dake karamar hukumar Bassa a jihar.

Wani shugaban matasan kauyen mai suna Danjuma Auta ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa maharan sun far wa mata ne da yara kanana a kauyen.

Auta ya ce saboda yawan hare- haren da suke fama da su a kauyukan, maza da mata kan yi kaura daga gidajen su, sannan wasu su zagaye kauyen don gadin masu barci.

” Amma abin mamaki ne yadda maharan suka shigo garuruwan mu a wannan dare suka kashe mana mata da yara batare da Kowa ya sani ba sai dai gawan su da muka gani, gashi duk mun zagaye kauyen don gadin mutanen mu.

Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Terna Tyopev yace bashi da masaniya game da wannan hari.

Share.

game da Author