Jami’an tsaro sun datse dukkan manyan hanyoyin da ake bi a shiga filin jirgin sama na Murtala Mohammed, da ke Legas, domin a tabbatar da an bai wa Shugaba Muhammdu Buhari dukkan tsaron da ya cancanta.
Wannan tsatstsauran mataki da aka dauka ya kuntata wa matafiya da sauran fasinjojin jiragen sama daban-daban.
Sai da ta kai fasinjoji na sauka kasa su na yin tafiyar kasa ta kusan kilomita biyu kafin su karasa filin jirgi, don gudun kada jirage su rika tashi su na barin su a tasha.
Buhari ya Legas yanzu haka a wata ziyarar musamman da ya kai ta kwanaki biyu.
Yayin da wakilin PREMIUM TIMES ya ziyarci Babban Asibitin Ikeja da misalin karfe 5 na asubahin yau, ya yi arba da dandazon ‘yan sanda sun datse tashar motar Olowu, sun hana motoci motsawa.
Wasu fasinjoji da suka zanta da PREMIUM TIMES, sun bayyana cewa gaskiya an takura musu, kuma an shiga hakkin su, an kuma tauye musu ‘yancin su na walwala, domin kowa ai ya na da na sa uziri.
Musamman wani fasinja mai suna Kabir, ya bayyana cewa ai ba wannan ne canjin da suka zaba ba.
Kabir ya ci tafiya a kasa karcat, don gudun kada ya jira har sai an bude hanya tuni jirgi ya tashi ya bar shi a tasha.
Discussion about this post