Zazzabin Lassa ya yi ajalin mutane uku a Ekiti

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Ekiti Olurotimi Ojo ya bayyana cewa mutane uku sun rasu sanadiyyar kamuwa da zazzabin Lassa da suka yi a jihar.

Kwamishinan ya kuma hori mutane da su kwantar da hankalin su cewa hukumar gudanar da bincike kan hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) na binciken gano dalilin bullowar cutar da yadda za a iya dakile yaduwar sa.

Ojo ya kara da cewa gwamnatin jihar za ci gaba da wayar wa mutanen jihar kai kan yadda za su kiyaye daga kama cutar.

Sannan asibitocin kula da masu fama da cutar a jihar wanda ya hada da asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya, asibitin Oba Adejuyigbe da asibitin koyarwa na jiha duk dake Ado Ekiti za su ci gaba da kula da wadanda basu da lafiya da kuma wadanda suka kamu da cutar.

Share.

game da Author