An zargi Sanata Abdullahi Adamu da kitsa makarkashiyar tsige Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.
Sanata Obinna Ogba daga jihar Ebonyi ne ya yi wannan zargin tare da cewa ya na da kwararan hujjoji.
A zaman Majalisar na yau Alhamis ne Sanata Ogba ya gabatar da “shaidar” wata tattaunawa da ya ce Sanata Adamu ya yi da wasu mutane a matsayin yinkurin tsige Sanata Saraki da wasu shugabannin Majalisar.
Daga nan sai Sanata Ogba ya nemi Majalisa da ta binciki zargin da ya ke yi wa Adamu.
“Na tashi yau da safe domin na sanar da Majalisa wata makarkashiya da su Sanata Abdullahi Adamu ke yi na tsige Shugaban Majalisa. Kuma idan ba ku manta ba, cikin watan Janairu Sanata Misau ya ce wasu na kulla makarkashiyar tsige Sanata Saraki daga shugabanci.
“To a yau ni ina masaniyar cewa wasu mutane tuni sun yi nisa da kulla wannan shiri, domin su tarwatsa shugabancin wannan majalisa. Sun shirya bada kudi a gudanar da zanga-zanga. An ma fara raba kudaden, cikin wadanda za su yi zanga-zangar kuwa har da mata ‘yan kasuwa. Don haka ya kamata a gaggauta daukar mataki.
Daga nan sai Ogba ya tashi ya gabatar da takardun da ya ce su ne hujjojin sa, kuma ya ce a gaggauta bincike.
Mataimakin Shugaban Majalisa Sanata Ike Ikweramadu ne ya shugabanci zaman sannan ya ja kunnen duk masu son kawo cikas a majalisa da su guji yin haka.
Daga nan an mika batun a hannun kwamitin majalisa da ya bincika ya tabbatar da hakan ko akasin haka.
Discussion about this post