ZANGA ZANGA: Za mu sadaukar da rayukan mu saboda El-zakzaky – Mabiya Shi’a

0

Yau Litinin ne aka cika kwanaki 70 cur ana gudanar da muzaharar neman a saki shugaban mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim El-zakzaky da aka tsare tare da uwargidan sa tun cikin Disamba 2015.

A kullum masu zanga-zangar kan fito kan titinan Abuja kuma su na yin zaman-dirshan a Cibiyar Unity Fountain, inda masu neman a ceto daliban Chibok, #BringBackOurGirls ke zama.

Wasu da PREMIUM TIMES HAUSA ta zanta da su, sun tabbatar da cewa ko za a shekara daya nan gaba ba a saki jagoran na su ba, to su kuma komai ruwa da iska ba za su yi fashin yin muzahara da zaman-dirshan a Abuja ba.

Sun ce dama sun yi bankwana da garuruwan su, ba za su koma ba sai tare da jagoran na su.

Share.

game da Author