Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi kira ga deliget da su tabbata sun zabi ‘yan takara nagari a zaben fidda gwani da za ayi na jam’iyyar APC yay Asabar a Jihar Kaduna.
Ya ce gwamnati bata da ‘yan takara shafaffu da mai, duk wanda ya ci zabe za a ba shi ba tare da an nuna fifiko.
” Ina rokon ‘yan Kaduna da deliget da suyi zaben da zai haifar da mai Ido ba tumin dare ba.”
Gwamna El-Rufai ya ce Kada jama’a su yarda wani jami’in gwamnati ya ce musu wai gwamnati na da zabi a ‘yan takara, ” Duk wanda ya ci shine dan takarar gwamnati.”
Da ya yi tsokaci kan yadda ayyukan gyara jiha suka ci gaba bayan dakatar da ita da akayi na dan wani lokaci, gwamna ya bayyana cewa duk da majalisar dattawa taki amincewa bankin duniya ta ba Jihar bashin dala miliyan 300, wasu bankuna sun amince su ba ‘yan kwangila kudaden aikin, su kuma gwamnati su tsaya musu.
Discussion about this post