Gwamnatin jihar Benuwai ta bayyana cewa za ta yi gwanjon shanu da dabbobin da ta kwata daga hannun makiyayan da suka karya dokar hana kiwon dabobbi a fili a jihar tun daga shekarar 2017.
Kwamishinan yada labaran jihar Lawrence Onoja ya sanar da haka ranar Alhamis bayan kammala zaman kwamitin zartarwa na jihar a Makurdi.
Onoja ya kara da cewa gwamnati ta umurci ma’aikatan kudi na jihar da ta nada shugaban da zai jagoranci gwanjon dabbobin.
Ya ce gwamnati ta ba duk makiyayin da aka kwace masa dabobbi daga nan zuwa ranar 19 ga wannan watan da su biya kudaden taran da gwamnati ta nemi su biya ko kuma su kwana a ciki.
” Za mu fara siyar da dabobbin da masu shi suka ki biyan kudaden tara daga ranar 20 ga wannan watan.” Inji Onoja.