Wasu ‘yan kabilar Bachama dake zaune a kauyukan Lawaru , Dong, Nzoruwe, Pulum, Kodomti da Shaforon a jihar Adamawa sun bayyana cewa zasu maka rundunar sojin sama na Najeriya (NAF) kotun (ICC) kan kisar da suka zargi rundunar ta yi da suka je aikin kwantar da tarzoma kauyukan.
Kabilun sun zargi NAF da aikata kisa da tauye hakin mutanen su sannan da mara wa Fulani baya a rikici.
” Muna da tabbacin cewa a ranar 4 ga watan Disambar 2017 rundunar NAF ta yi amfani da jiragen sama inda suka yi ta harbo bamai-bamai kan wasu kauyuka na mutanen mu.
Mai magana da yawun kungiyar Lawrence Jonathan ya ce ‘yan Bachama sun yanke shawarar maka rundunar Sojin saman ICC ne ganin kin sauraren su da suka yi.
Bayan haka jami’in hulda da jama’a na rundunar sojin sama Olatokunbo Adesanya, ya musanta wannan zargi.
” Tabas mun yi amfani da jiragen sama wajen kwantar da tarzoma a kauykan Numan amma ko da wasa jiragen mu basu harba bam kauyukan da wadannan mutane ke magana a kai ba.”