Za mu haka rijiyoyin banruwa 1000 domin noman rani a jihar Sokoto – Tambuwal

0

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatin sa za ta haka rijiyoyin banruwa 1000 don bunkasa noman rani a shekarar bana a jihar.

Tambuwal yace yin hakan ya zama dole ganin cewa dam din da ake amfani dashi wajen ban ruwa yayi wa manoma kadan, wato ba zai ishe su ba wanda dalilin haka ne ya sa gwamnati ta yanke shawarar gina wadannan rijiyoyi.

Bayan haka Tambuwal ya kara da cewa gwamnati ta kashe Naira miliyan 64 wajen siyan garman huda biyar, injinan markaden tumatir 50, injinan sarrafa shinkafa 40 sannan da taraktoci biyar domin inganta aiyukkan noma a jihar.

Daga karshe ya ce manoma 1,786 sun fara aiki da dabarun siyar da amfanin gona kamar su shinkafa, dawa da tumatir a shirin ayyukan noma na FADAMA III.

Ya ce a yanzu haka manoman dake cikin shirin FADAMA III a jihar sun kai 24,546 wanda 21,631 daka ciki maza ne sannan 2,915 matane.

Share.

game da Author