Za a yi wa yara 900,000 allurar rigakafin bakon dauro a Enugu

0

Jami’in ma’aikiatar kiwon lafiya na jihar Enugu Okechukwu Ossai ya bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin yi wa yara kanana allurar rigakafin cutar bakon dauro.

Ya sanar da haka ne ranar Juma’a inda y ace suna sa ran cewa yawan yaran zai kai kashi 20 bisa 100 daga cikin adadin yawan yaran da za a yi wa allurar.

Ossai ya ce za a yi wa yara ‘yan watanni tara zuwa shekara biyar ne allurar a duk cibiyoyin kiwon lafiya da sauran wurare a jihar daga ranar 8 ga watan Maris zuwa 20.

Ossai ya yi kira ga iyaye da su tabbata sun kai ‘ya’yan su allurar rigakafin da zaran an fara.

Share.

game da Author