Shugaban kungiyar manoman shinkafa (RIFAN) reshen jihar Zamfara Ishaq Ajiya-Anka ya bayyana cewa domin bunkasa aiyukan noman rani a kasar nan gwamnatin tarayya ta amince ta raba wa manoman shinkafa 40,000 kaya da na’urorin ayyukan noman rani a jihohin Zamfara da Kebbi.
Ajiya-Anka ya sanar da haka ne ranar Litini inda ya kara da cewa manoma 5,403 a jihar Zamfara za su karbi nasu a cikin wannan mako da muke ciki.
” Za mu raba wa manoman iri, takin zamani (NPK da Urea), maganin feshi, goran feshi da injin ban ruwa a Gusau, Shinkafi, Bukkuyum, Dansadau da Talatan-Mafara.”
Ishaq ya ce rashin samun katin da zai bambamta manoman da ya kamata a ba ne ya hana su raba kayan aikin amma da zaran an kammala tantancewar za su fara rabon kayan.
A karshe shugaban kungiyar reshen jihar Kebbi Sahabi Augie ya ce manoman shinkafa 39,000 ne za su amfana daga wannan rabo.