Za a fara kula da masu fama da cutar tarin fuka kyauta a jihar Oyo

0

Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Oyo Azeez Adeduntan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince a fara kula da masu fama da cutar tarin fuka kyauta.

Ya sanar da haka ne ranar Lahadi a taron ranar cutar wanda ake yi duk shekara a watan Maris.

Ya ce kula da masu fama da cutar tarin fuka kyauta kokari ne na gwamnan jihar Abiola Ajimobi domin dakile yaduwar cutar a jihar.

Ya ce yin haka ya zama dole musamman yadda bincike ya nuna cewa Najeriya na cikin jerin kasashe 22 a duniya dake fama da cutar tarin fuka.

‘‘Ita dai wannan cutar ana iya kamuwa da ita ne idan ana yawan kusantan wanda ke dauke da ita, idan mai dauke da cutar na yawan zubar da yawu a fili, yawan yin tari cikin mutane ba tare da rufe baki ba.”

A karshe Adeduntan ya ce gwamnati ta umurici duk asibitocin dake fadin jihar cewa daga yanzu za su fara yin gwaji da bada maganin cutar tarin fuka kyauta wa duk wanda ke bukata.

Share.

game da Author