‘Yar kunar bakin wake ta tada bam a Buni Yadi, Jihar Yobe

0

Wata ‘yar kunar bakin wake ta kashe kan ta sannan wasu mutane uku sun sami rauni sanadiyyar tada bam din da ta yi a Buni Yadi jihar Yobe.

Wani da abin ya faru a idanuwar sa ya bayyana cewa bam din ya tashi ne bayan an idar da sallar asubahin ranar Juma’a a mazabar Fulatari, Buni Yadi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya ta rawaito cewa mutane ukun da suka sami raunuka na samun kula a asibiti yanzu haka.

Share.

game da Author