‘Yan sanda sun arce da wakilin mu zuwa Kano – Daily Trust

0

Kamfanin jaridar Daily Trust da ke da hedikwata a Abuja, ya bayyana sanarwar cewa jami’an ‘yan sanda daga Kano sun yi tattaki har Abuja, sun kama wakilin jaridar a Majalisar Tarayya, mai suna Musa Abdullahi Krishi.

Sanarwar wadda Babban Editan jaridar, Mannir Dan-Ali ya sa wa hannu, ta ce an kama shi ne wajen karfe 11:30 na ranar yau Talata kuma aka wuce da shi Kano.

YADDA AKA KAMA SHI

An kama shi yau Talata da misalin karfe 11:30, ranar 13 Ga Maris, 2018. Sun bayyana masa cewa daga Shiyyar Yan sanda ta Daya da ke Kano su ke.

Sun saka shi a cikin mota kirar Hilux mai lamba ABJ RSH 850 AH. Daga ofishin DPO na Majalisar Tarayya suka kai rahoto daga nan jami’an ‘yan sanda shida a cikin farin kaya da suka ce daga Kano aka turo su, su tafi da shi a yi masa tambayoyi.

MUSABBABIN KAMA SHI

Duk da dai ba su fadi dalili ba, kama Krishi na da nasaba da buga wata talla da Daily Trust ta yi a ranar 26 Ga Janairu, 2018, wadda ba ta yi wa Gwamnan Jihar Jigawa, Badaru Abubakar dadi ba.

Ga irin yadda aka jami’an ‘yan sanda suka rika yi wa Daily Trust barazana da kuma irin sa-tok-sa-katsin da muka rika yi da su, har tsawon wata daya da rabi:

1 – An buga wata talla a ranar 26 Ga Janairu, 2018, wadda wata kungiya mai suna ‘‘Coalition of Muhammad Badaru Abubakar Support Groups suka biya kudi aka buga musu. Tallar na kunshe da wasu hotuna inda ke nuna Badaru tare da tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo.

2 – A ranar da aka buga tallar sai lauyoyin Gwamna Badaru suka rubuto wasika suka ce Badaru ya nesanta kan sa da wannan talla, don haka a buga cewa gwamnan ya barranta da tallar.

3 – To a ranar 28 Ga Janairu, 2018, mun buga a cikin Daily Trust cewa Gwamnatin Jihar Jigawa ta nesanta kan ta daga wannan talla.

4. Sai kuma ranar 5 Ga Fabrairu, 2018, Daily Trust ta buga bayanin bada hakuri kamar yadda lauyoyin gwamnan suka nema a yi.

5. Cikin watan Fabrairu, sai Daily Trust ta samu wasika daga rundunar ‘yan sanda ta Kano, suka ce sun fara gudanar da binciken yadda aka buga wannan talla. Sun kuma hado har da sammamce daga alkalin kotun Majistare a Kano, amma sammacen ba ya dauke da sunan wanda ke kara, kuma babu lambar ko shi me sammamce na nawa da kotun ta fitar.

6. Mun gabatar musu da dukkan bayanan da suke nema da za su yi binciken su a kai. Amma duk da haka ba su gamsu ba, sai ‘yan sanda suka gayyaci hukumar gudanarwar Daily Trust zuwa Kano domin karin bincike.

7. Ganin yadda wannan matsala ce mai sauki wadda ba aikata mummunan laifi ba, amma ta dauki sabon salo, sai Daily Trust ta rubuta takardar korafi ga Sufeto Janar na Kasa, a ranar 15 Ga Fabrairu, 2018, aka nemi ya shiga tsakani.

Shi kuma ya nada kwamiti na masu bincike a Abuja ya ce su bincika su je masa da bayani.

DA HANNUN GWAMNA BADARU A KAMA KRISHI

To abin ya ba Hukumar Gudanarwar Kamfanin Daily Trust mamaki, ganin yadda ‘yan sandan Kano suka bijire wa umarnin Sufeto Janar, suka yi gabagadin kame wakilinmu su gudu da shi zuwa Kano. Mun yi amanna da cewa ‘yan sanda ba za su aikata haka ba, sai da fuskantar matsin-lamba daga gwamnatin jihar Jigawa.

Mu na kallon wannan bi-ta-da-kulli a matsayin wata barazana ga ‘yan jaridar da ke aiki a Daily Trust da jaridar dungurugum. Kai ba ma mu kadai ba, har ma da aikin jaridar bakidayan sa. Abin da aka buga ba fa wani cin-fuska ko bata-suna ba ne ga gwamnan jihar Jigawa ko ga wani dan siyasar da abin ya shafa.

Mun bi yadda suke so da lalama, domin mun janye tallar kuma mun bada hakuri ga gwamnatin jihar Jigawa. To arcewa da wakilinmu da aka yi zuwa Kano abin da ba za mu lamunta ba ne, kuma tauye masa ‘yanci ne. Hakan na nuna cewa akwai wata makarkashiyar karkatar da Daily Trust daga gudanar da aikin ta da dokar kasa ta ba ta damar gudanarwa, na bai wa kowane dan Najeriya damar fadar albarkacin bakin sa a cikin jaridar, dangane da batutuwa na dimokradiyya.

Don haka mu na kira da a gaggauta sakin wakilinmu Musa Abdullahi Krishi da gaggawa. Kuma mu na neman rundunar ‘yan sanda ta Kano ta ba Daily Trust hakuri. Mu na kuma kira ga Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari su ba ‘yan sandan Kano umarni su saki wakilin mu da gaggawa, su dauko shi, su maida shi Majalisar Tarayya inda suka same shi ya na aiki suka arce da shi.

Wani bincike da PREMIUM TIMES HAUSA ta gudanar a yau cikin gaggawa, ya nuna cewa duk da irin sukar da jam’iyyar APC ta rika yi wa gwamnatin Goodluck Jonathan dangane da cin zarafi ko kama ‘yan jarida, to hawan APC mulki a cikin watanni 30, an kama ‘yan jarida masu yawan gaske.

Idan ba a manta ba, daga cikin wadanda aka kama a hawan mulkin Buhari, akwai Shugaban Kamfanin jaridar PREMIUM TIMES, Dapo Olorunmi, Shugaban Sahara Reporters, Sowore, Babban wakilin Daily Independent a Abuja, wakilin Vanguard na jihar Kaduna da sauran su.

Share.

game da Author