Gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya bayyana cewa ‘yan gudun hijira sama da 4,000 daga jihar Benuwai na samun mafaka a jihar.
Ya fadi haka ne a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar ranar Alhamis.
Lalong yace mafi yawan ‘yan gudun hijiran dake samun mafaka a jihar ‘yan kabilar Tiv ne da Fulani wadanda rikicin makiyaya da manoma ya ritsa da su kuma suka rasa muhallin su.
Ya kuma kara da cewa bayan wadanda suka taho daga Jihar Benuwai, akwai wasu yawa daga jihohin Adamawa, Barno, Yobe, da Jihar Kaduna.
” Tun da ‘yan gudun hijira suka fara tururuwa daga wadannan jihohi zuwa jihar Filato, babu tallafi da ta taba samu daga gwamnatin tarayya haka kuma ko daga jihohin da suke tahowa daga. A dalilin haka muke rokon gwamnati da ta kawo mana dauki kan haka.”
A karshe Lalong ya yaba wa Buhari kan matakan da ya dauka wajen shawo kan rikice-rikicen da ake fama da su a kasar nan.
Discussion about this post