Hukumar kula da ‘yan gudun hijira na kasa da kasa (NCFRMI) ta bayyana cewa za ta dawo da ‘yan gudun hijira 91,000 ‘yan Najeriya da ke samun mafaka a kasar Kamaru.
Jami’in hukumar Lawal Hamidu ya shaida wa manema labarai cewa kasar Kamaru za ta dawo da wadannan ‘yan gudun hijira ne bisa ga yarjejeniyar da ta yi da Najeriya.
Hamidu ya ce kasar Kamaru ta tsara shiri don ganin cewa wadannan ‘yan gudun hijira sun dawo kasar su cikin koshin lafiya.
” Cikin ‘yan gudun hijiran 91,000 din da za a dawo da su 4,000 daga jihar Adamawa suka fito sannan 87,000 daga jihar Barno.”