Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki, ya samu nasarar hayewa kan kujerar mulkin majalisa, a wani yanayin kutunguila da algungumacin siyasa. A gefe daya kuma, hawan sa shugabancin bai yi wata-wata ba, sai ya nuna salon mulkin dannau zai yi, duk wanda ya danne ko ya take, to ya taku kuma ya dannu.
Da ya ke ya iya tuggun siyasa, kamar mahaifin sa, marigayi Olusola Saraki, wanda shi ma ya yi shugabancin Majalisar Dattawan a Jamhuriya ta biyu, lokacin mulkin Shehu Shagari, sai ya kasance abin kamar a nono ya sha – wato abin nan da Bahaushe ke cewa, ‘barewa ba ta gudu dan ta ya yi rarrafe. (Premium Times Hausa)
Bai wani bata lokaci ba, sai ya fara nuna maitar sa a fili, tun ya na yi a boye, Saraki ya jaddada mulkin ‘yan karambosuwa da karfa-karfa. Ya yi haka domin gwanin kitimirmirar siyasa ne, ta yadda ya gina doguwar katanga ya kange Majalisar Dattawa daga Jam’iyyar APC da Shugaba Muhammadu Buhari, yadda ko leken cikin ta ba su iya yi, ballantana har su jefa kafa ciki su rika yi masa katsalandan.
Ya nuna cewa shi dattijon da ya iya fadan gurugubji, wato fada da tsarar sa dattawan jam’iyya, shugaban kasa da duk wani kushegeren mamba na majalisar dattawa. Fadan dattawa ba a kuka ko zubar da hawaye, sai dai wanda ya ji naushi a hanci ya fyace. Shi kuwa Saraki hatta rugumutsin da ake ta tafkawa da shi a gaban alkali, bai taba yin ko gezau balle ya fyace ba. Jure dafi sai bauna!
Sanatoci uku da su ka nemi lakutar masa hanci da yatsu, tun ba su kai ga cewa kulle ba, ya karya musu yatsu, tilas su ka saduda. Saraki ya nuna Majalisar Dattawa cewa shi fa gwangwala ce, a hau ki a zame, ki hau mutum ki zauna daidai.
Irin karankatakaliyar da kamtsa kafin ya zama shugaban majalisar dattawa ta isa a yarda cewa Saraki goga ne mai nike wa shanu turba – ka na gaba shanun ka biye.
Duk wata kisisina da kullen-kullen sai Sanata Ahmed Lawan ya zama Shugaban Majalisa, hakan bai yi nasara ba kamar yadda shugabannin jam’iyyar APC su ka nemi yi. Yayin da aka baje kujerar a faifai aka daka wasoso, sai ga tsokar naman gaba dayan ta a cikin bakin Bukola Saraki. Gafiya tsira da na bakin ki!
Bayan kura ta lafa aka duba aka ga Ahmed Lawan da shi da magoya bayan sa ko kasusuwa ba su samu ba. To Saraki dama rikakken dan kokawa ne, amma duk da haka a wannan ranar sai da ya hada da sojan-haya, Ike Ekweramadu, ya samu ya yi musu mai shal.
Ba da dadewa ba Saraki ya zame wa majalisa karfen kafa, ta yadda ko ta ina aka motsa, ba a maganar kowa sai maganar sa. Babu wani batu, mai dadi da maras dadi, sai batun da ya shafi Saraki. (Premium Times Hausa)
A bangare daya kuma, duk wani kokarin a tube shi an yi, ba a yi nasara ba. An maka shi kotu, har yanzu shiru. An tayar masa da cida mai rugugi, amma ko razana bai yi ba, balle ya gudu ya shige daki, kada aradu ya fada masa.
BARDE BA A HAYE MAKA:
Hawan sa shugabancin majalisa bai yi wa shugabannin APC dadi ba, musamman uban tafiyar jam’iyyar, Bola Tinubu. Babu abin da Tinubu bai yi ba, domin ya tabbatar an sake zabe, an kayar da Saraki, amma ko kusa ba labari.
Da ya ke Saraki mai wayau ne, yayin da ya cika bakin sa da tsokar naman da ya raruma a tsakiyar majalisa, sai ya rika cizga ya na samma zaratan da suka taya shi kokawa. Haka ya rika ba ‘yan-gaban-goshinsa mukaman shugabancin kwamiti-kwamiti masu romo da kuma bargon tsotsa. Ko ka na APC ko PDP, matsawar ka taya shi fizgar nama, to kai ma sai an ci tare da kai.
Haka aka rika tafiya, Saraki ya zama duwawu, dole gwamnatin APC ta zauna da shi. A matsayin sa na mutum mai mukami na uku a Najeriya, bayan Buhari da Osinbajo, sai Saraki ya zama abin da Hausawa ke cewa, ‘tilas a ci kasuwa tare da makiyi.’ Haka za a rika haduwa a wurin taro ko fadar gwamnati ana kallon-kallo tsakanin Shugaban Kasa da Shugaban Majalisar Tarayya.(Premium Times Hausa)
Ba a nan ya tsaya ba, sai da ya tabbatar da cewa babban gogarman sa, Sanata Ali Ndume shi ne ya zama Shugaban Masu Rinjaye. Sai dai kuma Ndume ya gamu da gamon sa a lokacin da ya zakalkale wa Saraki, ya nemi Majalisa ta yi bincike kan wani rahoto da ke da nasaba da batun kin amincewa da shugaban EFCC, Ibrahim Magu.
YADDA YA DAMALMALA NDUME
Yayin da Ndume ya fito karara ya nuna goyon bayan sa ga shugaban riko na EFCC, Ibrahim Magu, wanda suka fito daga jiha daya, nan take ya raba hanya da Saraki da ‘yan-karankatsagallin Saraki. Kura ta tirnike, har aka tsige Sanata Ndume daga Shugaban Masu Rinjaye, aka nada Ahmed Lawal.
An yi wa Ndume bi-ta-da-kulli yayin da ya tsoma bakin sa a sha’anin zargin Saraki bai bayyana yawan kadarorin sa ba, inda ya ce jaridu sun nemi a binciki Saraki. Wannan ya kai ga an dakatar da Ndume daga majalisa, kuma tilas ya hada kayan sa ya fice.
ISHARA GA ABDULLAHI ADAMU
Daya daga cikin karin karfin da Saraki ya samu a majalisa shi ne kyakkyawar alakar sa da sanatocin da a baya sun taba yin gwamnoni kamar sa kenan. musamman ma Sanata Abdullahi Adamu, tsohon gwamnan jihar Nassarawa, wanda Saraki kan kira shi ‘yayana’, ko kuma ‘uban kasa.’
Duk wannan dadin bakin bai hana Saraki wasa zarto ya gigara wa kujerar da Adamu ke takama da ita, ta shugaban kungiyar Sanatocin Arewa ba, a lokacin da ya nemi ya shige wa Saraki hanci.
Adamu ya nuna rashin amincewa da gya dokar zabe, shi da wasu gungun sanatoci, su na cewa makarkashiya ce ake so a yi wa Buhari. Wannan rudani ya janyo an yi wa Adammu terere a duniya, inda aka ce an tsige shi saboda ya ci kudin kungiya har naira milyan 78, wadanda ya ce wai a gona ya boye su, amma wasu birai suka yi watandar kudaden gaba dayan su. (Premium Times Hausa)
A halin yanzu an shata layi, Adamu ya zama cikakken dan adawar kokarin taka wa Saraki burki. Tuni dai ake kallon Adamu ba zai iya jure karo-da-karo da Saraki ba, domin a ganin wasu, kahonnin sanatan ko kadan ba su kai na Saraki kwari ba.
TAKA WA OVIE OMO-AGEGE BURKI
Sanata Ovie Omo-Agege na daya daga cikin sanatoci 9 da suka yi wa Saraki tawayen kin amincewa a sauya ranakun zabe. Ya fito ne daga shiyyar tsakiyar jihar Delta. Ya tashi ya nemi a ba shi damar yin magana, amma Saraki ya nuna masa ya zauna ya yi wa mutane shiru. Danganta sauya ranakun zabe da makarkashiya ga shugaban kasa da su Omo-Agege suka yi, ya janyo masa tsangwama da dora masa karan-tsana.
Kwanaki kadan sai Dino Melaye ya yi nuni da wani jawabi da Omo-Agege ya yi, ya nemi a yi bincike, kuma aka amince kwamiti ya binceke shi.
DINO MELAYE: GOGARMAN SARAKI
Sanata Dino Melaye ne a sahun gaban goyon bayan Saraki duk rintsi. Ko kotu Saraki zai je, bai taba barin Melaye a gida ko a ofis ba. Ko lokacin da EFCC su ka gayyaci Doyin, matar Saraki, Melaye ne babban dan rakiyar ta. (Premium Times Hausa) Baya ga wannan, Melaye ne kanwa-uwar-gamin da ya shugabanci kwamitin binciken Sanata Ndume, kuma shi ne a sahun gaban kitsa yadda aka tsige Abdullahi Adamu daga shugabancin kungiyar Sanatocin Arewa.
Discussion about this post