Yadda Sanata Dino ke loda mana kudi sannan yana siya mana bindigogi – ‘Yan ta’adda

0

Wasu ’yan ta’adda da kisa da aka kama da manyan bindigogi da sauran muggan makamai sun bayyana wa ’yan sanda cewa Sanata Dino Melaye ne ke ba su makaman, kuma shi ke daukar nauyin su.

Wannan furuci dai ya kara dagula mummunan rikicin siyasar da ke tsakanin Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi da kuma Sanata Dino Melaye, shi ma daga jihar Kogi.

Wani jawabi da Kakakin Rundunar yan sanda na kasa, Jimoh Moshood ya fitar, ya bayyana sunayen ’yan-ta-kifen na Dino Melaye da cewa su biyu ne aka kama, akwai Kabiru Saidu da kuma mai suna Nuru Salisu. An dai gabatar da su ne a gaban manema labarai a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda Mosheed, ya ce jamai’an tsaro suka kama su da makamai ciki har da bindiga samfurin AK-47.

Mosheed yace wannan zargi da ake yi masa ne ya sa a baya jamai’an tsaro suka rika farautar sa.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda a cikin makonni uku da suka gabata, ‘yan sanfa suka ritsa Diino Melaye a cikin kotu, shi kuma ya ki fita har bayan 7:30.

A lokacin Melaye ya zargi gwamnan Kogi Yahaya Bello da kitsa matsa sharri, inda shi ma Yahaya Bello ya ce bau ruwan sa, kawai dai munanan laifukan Dino ne da ya aikata ke bibiyar sa.

An dai kama Saidu mai shekau 31 da kuma Salisu mai shekaru 25 a ranar 19 Ga Janairu, kuma sun furta da kan su cewa sun sha kama jama’a su na garkuwa da su, kuma sun sha aikata fashi a garuruwa daban daban na cikin jihar Kogi.

An cafke su bayan an yi ta musayar wuta har sa’o’i da dama a Ogojueje da ke cikin karamar humumar Dekina ta jihar Kogi.

An kuma kai shekara biyu ana neman su ruwa a jallo, sai wannan karo aka cafke su.

Saidu yace wani dan Tsohon Gwamnan Kogi mai suna Mohammed Audu ne ya gabatar da shi ga Dino Melaye. Mohammed da ne ga Abubakar Audu.

Daya daga cikin su shi ne aka kama ya fallasa tattaunawar sa da Dino Melaye, dangane da yadda suka kulla wa wani jami’in gwamnatin Kogi sharri cewa ya yi kokarin halaka Dino Melaye.

Sun ce a cikin Motar Dino Melaye suka zauna suka shirya komai, a kan titin zuwa filin jirgin saman Abuja a cikin Disamba, 2017.

“Sun ce Dino ne ya dauke su haya, kuma ya ce su dauko wasu sojojin hayar, domin su yi masa aiki, tunda ga zabe ya gabato. Ya na so su rikita jihar Kogi, kuma su yi maganin masa aiki a kan ‘yan adawar sa, a zaben 2019.”

Sun ce bayan sun gama ganawar sirrin, ya dauki kudi naira N430,000 ya hada musu da bindigogi uku ya ba su.

Jami’an tsaro sun ce, bayan sun kammala bincike, a ranar 2 Ga Maris, sun rubuta wa Shugaban Majalisar Dattawa, Bukula Saraki wasika, domin su na bukatar Dino tambayoyi. Maimakon haka, sai Dinon ya bata al’amarin dalilin neman sa da suka rika yi su cafke shi kenan.

Wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa Saraki ya maida wa jami’an ‘yan sanda amsar wasikar su. An mika kwafen ta ga Mataimakin Sufeto Janar Joshak Habila, kuma aka yi kwafe ga Sufeto Janar na Najeriya.

Yayin da aka shigar da Dino Melaye kara a kotun Lokoja shi da Mohammed Audu, shi kuma Dino ya ce duk sharri ne kawai aka yi masa da kazafi kawai.

Share.

game da Author