Yadda masu garkuwa suka sace mahaifiyar ‘Shema Oil’ Hajiya Diya a Katsina

0

A ranar Juma’a ne kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina Gambo Isah ya sanar cewa an sako Hajiya Diya Abdullahi mahaifiyar Nagogo Mamman, mamallakin Kamfanin Shema Oil.

Hajiya Diya, na da shekaru 85 ne a duniya.

Idan ba a manta ba a ranar Juma’ar da ta gabata ne wasu masu garkuwa suka sace Hajiya Diya a cikin gidan ta dake a karamar hukumar Dutsen Ma dake jihar Kastina.

Bayanai sun nuna cewa masu garkuwan sun harbi wani Usman Barkiya sau biyu da bindiga yayin da ya zo kawo mata dauki amma Allah ya sa ya na da sauran kwana, yana kwance a asibiti ana kula da shi. Sannan masu garkuwan sun bukaci Naira miliyan 100 kafi su sako ta.

Isah ya bayyana cewa barayin sun sako Hajiya DiyaAbdullahi ne ranar Alhamis amma ba shi da tabbacin ko iyalen Mamman sun biya kudin fan sa ko a’a.

Ya ce ana sa ran za a kamo wadanda suka yi garkuwa da Hajia Diyya.

Share.

game da Author