Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya karyata furucin da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo yayi cewa wai gwamnatin sa ta barnata naira biliyan N100 da wasu dala miliyan $289 makonni kadan kafin zaben 2015.
Mai taimakawa tsohon shugaban kasa kan sabbin kafafen yada labarai Reno Omokri, a wata takarda da ya fitar ya bayyana cewa idan har abin da Osinbajo ya fadi gaskiya ne ya fadi wa duniya cewa hakanne ta hanyar fiddo hujjojin da zai tabbatar da gaskiyar sa.
” Ba wannan karon bane Osinbajo ya ke labta karya baro-baro, ya bari shaidan yana tasiri a zantukan sa yanzu domin kuwa maganganun sa kan zama shiririta ce kawai.
” Idan yan Najeriya basu manta ba, yabo maganganu da karerayi ne Osinbajo ya saba yi shekaru uku kenan da hawan su mulki. Bari in gaya muku gaskiya, Jonathan bai kashe naira biliyan 150 ba makonni biyu kafin zabe, idan kuma akwai shaidar yayi haka a baza shi a faifai kowa ya gani.

” Sannan kuma ba gaskiya bane cewa da yayi wai Jonathan ya kashe zunzurutun kudi har naira biliyan 14 domin bunkasa ayyukan noma a kasar nan cikin shekaru uku.
” Gwamnatin Buhari da bata wuce shekaru uku ba kan mulki ta ciwo bashin da jam’iyyar PDP ba ta ciwo ba a tsawon shekaru 16 da tayi tana mulki.
A dalilin wadannan hujjoji da ya zayyano, ya gargadi gwamnatin Buhari ta daina jingina gazawarta da gwamnatin Jonathan.