Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Kano Kabiru Getso ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnati ta aika da ma’aikatan kiwon lafiya domin gudanar da bincike kan menene sanadiyyar bullowar wata cuta da ba a san irin ta ba a karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar.
Ya sanar da haka ne ranar Talata a garin Kano inda ya kara da cewa sun yi haka ne domin gano irin cutar da kuma nemo yadda za a magance ta maza-maza.
” Mun gaggauta aikawa da masu gudanar da bincike kan cututtuka karamar hukumar Dawakin Tofa bayan mun sami labarin bullowar cutar da har yayi ajalin mutane takwas.”
Discussion about this post