WATA SABUWA: Yadda Ministan Kudi, Tsare-Tsare, Kiwon Lafiya suka kwashe biliyan 10 a asusun NHIS

0

Majalisar ta gayyaci Ministan Kasafin Kudi, Udo Udoma, ta Harkokin Kudi, Kemi Adeosun, na Lafiya Isaac Adebowale da kuma Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, da su bayyana su yi mata bayanin hakikanin gaskiyar yadda aka cire naira biliyan 10 daga asusun ajiyar Hukumar Inshorar Kiwon Lafiya ta Kasa, NHIS.

Wannan kwatagwangwama dai ta fito fili ne a jiya Laraba, bayan da majalisar ta gaiyaci Shugaban Hukumar wanda aka maida aiki kwanan baya, bayan an dakatar da shi.

Farfesa Yusuf Usman yayi bayanin cewa bai ga dalilin da za a dora masa alhakin salwantar naira biliyan 10 na NHIS ba, alhalin ba haka bane.

Daga nan sai Yusuf ya fara warware zare da abawa cewa:

“A da dai wannan naira biliyan 10 ta na cikin Asusun Bai-daya (TSA) na hukumar NHIS ajiye a Babban Bankin Tarayya CBN. Wata rana sai Ministar Kudi ta rubuto wasika, ta ce kamata yayi NHIS ta kasance wuri ne da zai rika samar wa gwamnatin tarayya kudin shiga.

“Ta rubuto min wasika, wadda a yanzu haka ina da kwafin cewa za a cire wadannan naira biliyan goma daga asusun NHIS, a bai wa gwamnatin tarayya.

“Kuma hakan ita Ma’aikatar Harkokin Kudin ta yi, ta cire kudaden tare da masaniyar Minstan Harkokin Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Ministan Kiwon Lafiya da kuma masaniyar Gwamnan Babban Bankin Najeriya.”

Yusuf ya kuma shaida wa kwamitin majalisa cewa kamfanonin MHO sun rike makudan kudade ta yadda kawai shi ya zama kamar wani ‘jami’in karbo bashi kawai.’

Idan ba a manta ba, Ministan Lafiya ne ya dakatar da shugaban na NHIS, kuma ya kafa kwamitin bincike.

Kafin sannan, an yi ta kai ruwa rana inda Yusuf ya rika zargin ministan da yi barankyankyamar kudade.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya maida Yusuf kan aikin sa, a bisa dalilin cewa kwamitin da ya bincike shi na da wata kullalliya a kasa, kuma an kasa kama shi da wani tartibin laifi.

Share.

game da Author