Jami’an tsaro na NIA sun shiga farautar Jakadan Najeriya a Chadi, sakamakon wata shaida da ya bayar ga Kwamitin Majalisar Tarayya a cikin watan da ya gabata.
Cikin shekarar da ta gabata ne dai gwamnatin tarayya ta kira Jakada Mohammed Dauda daga kasar Kamaru, ta nada shi shugaban hukumar NIA na riko, bayan korar dakatarwa da aka yi wa Babban Daraktan, Ayodele Oke.
An umarci Oke ya sauka a yi binciken yadda tulin kudin hukumar da aka samu a cikin wani gida a unguwar Ikoyi, cikin Legas.
Shi kuma Dauda ya rike a matsayin riko daga Nuwamba, 2017 zuwa Janairu, 2018, sai aka maye gurbin sa da Ahmed Rufai Abubakar.
Majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an umarci Dauda da ya koma matsayin sa na farko a kasar Chadi ya ci gaba da aikin da ya ke yi a can.
Dauda bai koma ba, ya bada dalilin cewa rayuwar sa a Chadi za ta shiga cikinn hadari, domin yanzu an nuna cewa shi tsohon jami’in tsaro ne na NIA a Najeriya kenan. Don haka ba zai iya aiki a matsayin jakadan Najeriya a kowace kasa a duniya ba.
Haka ya ci gaba da zaman sa, shi bai koma NIA ya ci gaba da aiki ba, shi kuma bai koma aikin sa na jakada a kasar Chadi ba, gudun kada a kashe shi, tunda an san ya taba yin aikin hukumar tsaro na NIA kenan.
“A wani bangaren kuma, wadanda ya ke zargi da wawurar kudaden hukumar NIA da ya fallasa a Majalisar Tarayya su ma su na tarkon sa.” Haka wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo labarin yadda Mohammed Dauda ya fallasa badakalar su Babagana Kingibe a lokacin da aka nada Kingibe shugabancin kwamitin da zai yi wa hukumar binciken yadda za a karfafa ta da inganta ta.
Lokacin da Kingibe ke aikin kwamitin, Dauda shi ne shugaban hukumar NIA na riko, kuma shi ne ya fada wa EFCC cewa Kingibe ya rika karbar kudade, har ma umarni ya bayar aka dankara wa wata farkar sa makudan kudaden kasar waje daga asusun NIA. Kingibe dai ya shaida wa EFCC cewa ba gaskiya ba ne, karya ake yi masa.
Majiya ta ce NIA na farautar sa ne kuma bayan da ya ki zuwa ya halarci kwamitin da aka kafa domin a ladabtar da shi, a bisa zargin sa da suke yi, ya zo da rana tsaka ya tona asirin hukumar, ya zubar mata da mutunci a idon jama’a.
Har lokacin da kae rubuta wannan labari dai ba a tantance ko an kama shi ba. Sai dai PREMIUM TIMES ta ga motocin jami’an tsaro guda biyu kusa da gidan sa, sun yi kwanton-bauna su na fakon sa, duk kuwa da cewa shi da iyalan sa duk ba su a cikin gidan.
An kuma wani jami’in tsaro a cikin kayan gida sanye da bakin gilashi, a kan kwanar shiga layin ya na dube-dube.