Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa, NEMA ta bayyana cewa ta karbi wasu ‘yan Najeriya su 149 da suaka dawo gida da Libya don kan su.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa wadanda suka dawo din sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed na Lagos a ranar Alhamis, a wani jirgin kamfanin Jirga-jirga na Buraq Airline, mai lamba 5A-DMG.
Jirgin ya sauka da misalign 10:45 na dare.
Daga cikin su akwai maza 197 da kuma mata 37
Manajan Kula da Harkokin ‘Yan Gudun Hijira na Kasa da Kasa a Lagos, Abraham Tamrat, ya gode wa kungiyar da kuma Kungiyar Tarayyar Turai saboda taimakawa da suke yi ana jigilar dawo da ‘yan Najeriya wadanda suka makale a Libya, kan hanyar su ta zuwa kasashen Turai.
Daga nan ya damka su ga jami’in kula da agajin gaggawa na Shiyyar Kudu Maso Yamma, Yakubu Sulaiman.
Daga nan sai yay i wa wadanda suka dawo din nasiha da cewa su daina yi wa kasashen Turai kallon tudun-mun-tsila, sau da yawa kallon kitse ake yi wa rogo shi ya matasan mu masu tafiya Turai ke karewa a cikin kangin bauta da sauran wahalhalun da a nan gida ba za su taba shan su ba.
Tamrat ya ce kusan kowace kasa na fama da na ta kunci ko matsalar tattalin arzikin, kamar yadda kasar su ke fama.
Discussion about this post