Jami’an ‘yan sanda masu kai wa ‘yan fashi da makami farmaki, sun ritsa Sanata Dino Melaye a cikin Babbar Kotun Tarayya a Abuja, da nufin cafke shi.
Dino Melaye ya ki yarda ya fice daga cikin kotun, gudun kada ya jefa kafa a waje su damke shi.
Laifin Dino Melaye shi ne kantara wa hukumar ’yan sanda karya da ya yi, ya ce wani jami’in gwamnatin jihar Kogi ya dauki nauyin kai masa hari a kashe shi. Alhali kuma karya ya ke yi.
An dai bayar da belin Dino Melaye a kan naira 100,000.00. To sai dai kuma jami’an ‘yan sanda dauke da manyan bindigogi sun zagaye kotun, su na jiran ya fito su damke shi. PREMIUM TIMES ba ta iya jin hakikanin dalilin da ya sa jami’an tsaro su ka yi wa Sanata Melaye kwanton bauna a bakin kotun Maitama ba, amma dai tabbas sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa zaman jiran sa kawai su ke yi da ya fito su dirar masa, tun da ba su da ikon kutsa kai cikin kotun su kama shi.
Sai dai kuma suna ta kafa tarkon su a waje, ashe shi gogan naka yana ta shirya yadda zai kauce ne. Kafin sun anakara an nemi shi an rasa. Ashe ya sulale ya ware.
An yi kokarin jin ta bakin lauyan Dino Melaye, Ricky Tarfa, wanda shi ne ya tsaya masa a shari’ar zabga wa kasar sa Najeriya karya da ya yi, amma ba a same shi ba.
Kafin Dino ya kauce, a inda yake labe a cikin kotu, ya tura sako ta shafin sa na tweeter cewa gwamnan Kogi Yahaya Bello ne da magautan siyasar Dino din ke masa bi-ta-da-kulli.
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin gwamnan, Gbenga ya ce gwamnan bai ma san abin da ake ciki ba.