TSOKACI: Fantsamar ‘yan Arewa masu jari-bola da yara ‘yan ‘shushana’ a Abuja

0

Wanda duk ya dade zaune a cikin Abuja, walau ma’aikacin gwamnati, ko dan kasuwa ko mai wata hidimar kan sa ko hidimta wa wani, ya san akwai matasa ‘yan Arewa masu sana’ar wanke takarma. Da ya ke yawanci duk Hausawa ne, a kan kira su da ‘shushana’, ko ‘shoe shina.’ Wannan duk bai hana kabilu da dama su rika kiran su ‘Malam’ ba, kamar dai yadda ake kiran duk Bahaushen da aka raina.

Wadannan masu wankin takalmi, watau ‘shushana’, dabi’ar su ita ce su tashi da sanyin safiya su na bin titi-titi da layuka, su na karkada dan akwakun da suke ajiye tarkacen wanke takalmi da goge shi a ciki.

Amma kuma da rana ta take sai ka neme su ka rasa, saboda dama yawanci masu bayar da takalma ana wankewa, suna bayarwa ne da safe kafin su fita ofis.

Sai dai kuma wani abin daure kai shi ne yadda tun daga cikin farkon shekarar 2017 ake samun kwararar yara masu ‘shushana’ kanana da wasun su ma ba su kai shekaru 16 ba.

Sannan kuma gaba dayan yaran nan kanana, duk Hausawa ne, ko a ce Hausa/Fulani, kuma da wuya ka ji wanda ya kammala firamare ko karatun addinin musulunci da zai iya tutiyar sanin hagun sa ko damar sa da su.

Kananan yara za ka gani, wasu daga garuruwan jihar Kebbi, wasu daga Zamfara, Sokoto, Jigawa, Katsina da wasu jihohin Arewacin kasar nan. Da yawan su ko magana kawai suka yi, z aka gane wannan daga Gumel ya ke, do Daura, ko Sanyinna, ko Dankama ko Tambuwal, Kaburma, Maru ko Argungu.

Abin dubawa a nan shi ne, idan ana kallon yawan irin wadannan yaran, sai mutum ya yi tunanin cewa lallai har yanzu an bar Arewa a matsayin koma-baya a kowace fuska. Sai ka ma kasa tantance yawan ratar da yara masu zuwa makaranta su ka yi wa wadanda ba su zuwa makarantar – idan ma har sun fi su yawa din.

Duk wata karamar sana’ar da ake yawon watangariyiya a kan titi a Abuja, to za ka ga yara ne ‘yan Arewa Hausa/Fulani. Ba safiya, ba rana, ba dare ba asubahi da yawa su na kan titi suna ’yan saide-saiden karkacen kayayaki.

‘Shushana’, dan Arewa. Turin ‘barrow’ a cikin kasuwanni, dan Arewa. Yankan farce, dan Arewa. Jari-bola, dan Arewa. Tallar rake, dan Arewa. Yalo da karas, dan Arewa. Kai duk wata talla da ka san ana farautar mai yin ta, a yi har a tarwatse a guje, to dan Arewa ne.

Sayar da katin waya a kan titi, maciya, dandali, bakin kantina, kulob-kulob da gidajen giya, duk yara ne ‘yan Arewa. Hatta masu bin karuwan kan titi su na sayar musu da kwaroron roba a tsakar talatainin dare, duk ‘yan Arewa ne. Arewa! Arewa!! Arewa dai!!!

Wani babban tashin hankali kuma shi ne fantsamar kananan yara da ba su wuce shekaru goma zuwa 13 ba, su na bi duk inda ake kasuwanci, bushasha ko sharholiya a cikin dare su na bara. Idan sun gan ka da shiga irin ta dan Arewa, to za su yi maka bara ne ka ba su don darajar Annabi (SAW). Idan a kofar mashaya ko gidan balle-bushasha su ka same ka, su zuga ka daidai yanayin halin da suka same ka don ka ba su kudi.

Babu abin da ban-tausayi kamar yadda matasan mu ‘yan Arewa su ke yawon jari-bola a Abuja da sauran garuruwan da ke kewaye da Abuja. Tun tsakar dare kamar karfe 12 ko karfe 1 su ke fara fita su na bin kwandunan tara sharar da ake ajiyewa kofar gidaje su na yamutsawa su tsinci abin da aka watsar.

Haka za ka rika jin karakainar su a kan titi har asubahi. Wasu ma ka ji karnukan cikin gidaje na ta yi musu haushi.

Sannan kuma wadannan matasan da yawan su ba ma a cikin hayyacin su su ke ba. Shi kan sa wurin kwanan su a cikin kangayen gine-ginen da aka yi can nesa da gari ya ke, ko kuma gefen wata shirgegyar bolar da kowane mai hankali ke kyamar bi ta wajen.

Shin irin wadannan yara kanana da matasa ‘yan Arewa, wai gwamnati ce ta bar su a baya, ko kuwa iyayen su ne suka bar su a baya? Ko kuwa ba su da iyayen da za su iya goya musu baya ne?

Share.

game da Author