Tsohon Minista, Hassan Lawal ya rasu

0

Hassan Lawal, tsohon ministan ayyuka da gidaje a lokacin mulkin marigayi Umaru Yar’Adua, ya rasu.

Ya rasu a tsakar daren Asabar a asibitin Turkish Nizamye da ke Abuja.

Kamar yadda iyalan sa su ka shaida wa PREMIUM TIMES, za a rufe sa yau Lahadi a garin su, Keffi, cikin jihar Nassarwa.

Kafin mutuwar sa, ya taba rike ministan kwadago, na kiwon lafiya da kuma ayyuka da gidaje.

Ya bar mata biyu da ‘ya’ya da ‘yan uwa.

Share.

game da Author