Tsohon gwamnan jihar Adamawa Abubakar Michika ya rasu a asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola.
Marigayi Michika ya rasu ne ranar Asabar bayan fama da ya yi da rashin lafiya.
Daya daga cikin ‘ya’yan sa Hafiz Michika ya koka kan yadda gwamnati tayi watsi da mahaifin su a lokacin da yake bukatar taimako, ” Sannan kwata-kwata ba a biyan sa fansho.”
” Gwamnan jihar Jibirilla Bindow ya ziyarci mahaifin mu jiya, sai dai kash ya zo a akan gaba, domin kuwa ciwon ta riga ta ci shi sosai. Kafin su iya yin wani abu akai Allah ya dauki abin sa.
Michika ya rasu ya na da ‘ya’ya 38, Maza 17, mata 21. Sannan yana da jikoki 99.
Ua yi gwamna a jihar Adamawa ne a jam’iyyar NRC, a 1992/93.