Mazauna sansanonin Fufore da Malkohi dake jihar Adamawa sun gudanar da zanga-zanga a sansanonin suna kokawa kan azabar tsananin yunwa da suke fama dashi.
Mazaunan wanda mafi yawan su matane da yara sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kawo musu dauki cewa rashin yin haka zai iya jefa su cikin matsanacin hali da kan iya sa su rasa rayukan su.
Wani cikin mazauna sansanin Malkohi daga jihar Barno mai suna Adamu Bukar da ke da mata daya da ‘ya’ya uku ya ce tun da aka basu abinci a watan Janairu ba a sake basu hakan ba har zuwa yanzu da yake magana da manema labarai.
Shima Haruna Bana ya ce idan har dai aka ci gaba a haka mutane musamman yara za su mutu saboda yunwa.
” Mu dai tun da hukumar NEMA ta raba mana abinci a watan Disambar 2017 ba mu sake samun wani abinci ba har zuwa yau din nan.”
Mazauna sansanonin da suka yi shekara biyu suna jira su koma garuruwan su sun yi kira ga gwamnatin jihar Barno da ta zo ta kwashe su.
Bayan haka daya daga cikin jami’an tsaron sansanonin wanda bai so a fadi sunan sa ba ya bayyana mana cewa lallai matsalar yunwan da ake fama da shi a sansanonin na iya haifar da matsala a fannin samar da tsaron da suke yi
” Dole ‘yan gudun hijiran suke fita nemo abinci saboda yunwan da suke fama da shi.”
Discussion about this post