TSANANIN YUNWA: An kai tirelolin abinci sansanonin jihar Adamawa

0

Hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA) reshen jihar Adamawa ta fara raba abinci wa mazauna sansanonin Malkohi da Fufore dake jihar.

Jami’in NEMA da ke kula da shiyar jihohin Adamawa da Taraba, Abbani Imam ya fadi a garin Yola.

Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne PREMIUM TIMES ta yi wani rahoto kan yadda mazauna sansanonin ke fama da matsanancin yunwa.

Idan ba a manta ba, Mazauna sansanonin Fufore da Malkohi dake jihar Adamawa sun gudanar da zanga-zanga a sansanonin suna kokawa kan azabar tsananin yunwa da suke fama dashi a makon da ya gabata.

Mazaunan wanda mafi yawan su matane da yara sun yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kawo musu dauki cewa rashin yin haka zai iya jefa su cikin matsanacin hali da kan iya sa su rasa rayukan su.

Wani cikin mazauna sansanin Malkohi daga jihar Barno mai suna Adamu Bukar da ke da mata daya da ‘ya’ya uku ya ce tun da aka basu abinci a watan Janairu ba a sake basu hakan ba har zuwa yanzu da yake magana da manema labarai.

Hukumar NEMA ta ce, akwai manyan motoci guda biyu da suka loda da abinci domin samar wa mazauna wadannan sansanoni.

Share.

game da Author