Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Kaduna, Ahmed Tsoho-Ikara, ya bayyana cewa har ya zuwa yau maniyyata 1,500 ne kacal su ka nuna aniyar zuwa Hajjin 2018 daga jihar.
Ya ce har yanzu akwai kujerar Hajji 5,000 da ake jira mai niyyar aikin Hajji ya biya kudi, amma shiru, ga shi kuma lokaci na ta kurewa.
Da ya ke nuna damuwar sa, ya ce wannan adadi na nuna cewa kashi 22.2 bisa 100 ne kacal suka fara biyan kudin kujera, su din ma ba duka kowanen su ya biya ba.
Tsoho-Ikara ya ce an ware wa jihar Kaduna gurabu 6,632, amma har yanzu ana neman maniyyata har 5,000, ga shi kuma ranar 30 Ga Maris, 2018 ne za a rufe karbar kudade da yin rajista.
Ikara ya bayyana wannan damuwa ce a Zariya, yayin da ya ke tattaunawa da wakilin Kamfanin Dillancin Labarrai na Najeriya (NAN).
“Tun cikin watan Nuwamba muka fara karbar kudaden ajiya daga mai niyyar zuwa aikin Hajji. Mun ce a rika ajiyewa da kadan-kadan, amma duk da haka jama’a ba su zuwa.”
“Daga cikin maniyyata 1,500 da suka fara biya, babu maniyyaci ko daya da ya biya kudin duka, naira miliyan 1.5. daga mai naira 800,000 abin da ya yi sama sai masu naira miliyan 1.2”
Daga nan sai ya bayyana dalilai kamar arha takyaf da amfanin gona ya yi. Ya ce manoma sun yi noma, amma amfanin gona ya yi arha. Manomi ba ya iya sayar da abin da ya sha wahala ya noma har ya samu biyan bukata.
Wani dalilin da ya kawo kuma shi ne tsadar da kudaden kasashen waje suka yi, darajar naira kuma karye.
Ya roki gwamnatin tarayya ta agaza wa Musulmi da Kiristoci masu bukatar zuwa aikin Hajji da ziyara Isra’ila.
Idan za a iya tunawa dai kafin hawan wannan gwamnati, ana biyan kudin tafiya aikin Hajji naira 800,000, amma sai kudin ya nunka zuwa miliyan daya da rabi tun daga bara.
Discussion about this post