AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Mutuwa kofa ce ta sabuwar rayuwa ga dan Adam, rayuwa ta dindindin, rayuwa mai bukatar guzuri. Mutum na tara guzurin sa ne a duniya. Da zarar mutum ya mutu to duk ayyukan lada sun tsaya sai abubuwa Uku: Sadaqa mai gudana, ‘ya’ya na gari da ilimi da ake amfani da shi.
Ruhin mamaci na kara daraja sakamakon kyawawan ayyukan da rayayyun mutanen duniya suka sadaukar ma mamaci da sakamakon biyan wasu basuka ko sakamakon sauke hakkokan da suka rataya a wuyar mamacin.
Ayyukan da mutum zai iya yi wa mamaci domin ladan ya isar wa mamaci sunada yawa. A takaice za mu ce dukkan ayyukan alhairi idan bawa ya kudiri sadaukar da ladan zuwa ga mamaci, Allah a cikin falalan sa zai karba kuma ya sadarwa mamacin da ladar, ta hanyar kawar masa da azaba (idan ya cikin halin azaba) ko daukaka darajar sa (idan yana cikin
halin Rahama).
KADAN DAGA CIKIN AYYUKAN DA ZA’A IYA SADAUKARWA MAMACI KUMA SU AMFANE SHI:
1. Addu’ah da Istigifari: yin addu’a da nemawa mamaci gafara shi ne babban abinda mamaci ke amfanuwa da shi.
2. Sadaka: yima mamaci sadaka, kamar bada taimako don gina masallaci ko makaranta da sunan mamacin, toh siyan hannun jari ne ga mamacin.
3. Layya: yima mamaci layya da sadakar da naman, shi ma daya ne daga cikin ayyukan da ke kai lada ga mamaci.
4. Hajji: yi ma mamaci aikin Hajji ga mutumin da be yi Hajji ba kafin mutuwar sa.
5. Karatun Al-Kur’ani: Sadaukar da ladan karatun Al-Kur’ani ga mamaci, bayan mai karatu ya karanta wani sashi sai ya ce: Ya Allah! kai ladan wannan karatu nawa ga………(wane).
6. Biyan Hakkin Allah: kamar Azumin farilla da Zakka, duk wanda ya mutu alhalin ana binsa (wani hakkin Allah) kamar Azumin farilla da Zakka idan aka yi a mamadin sa, toh, zai samu ladan aikin.
7. Biyan Hakkin dan Adam: duk wanada ya mutu alhali a kwai hakkin wani mahaluki a kansa, ba ya kwanciyar kabari har sai an sauke masa wannan hakkin.
Duk wani aikin alhairi da aka yi a mamadin mamaci kuma da niyyar Allah ya kai ladar aikin ga mamacin, toh Allah zai karba kuma ya sadar masa da ladar harma Allah ya shaida masa cewa WANE ne yayi maka aiki KAZA, ladar aikin ne ta daukaki darajar ka a wannan makwanci (Kabari), kamar yadda Imam Bukhari ya ruwaito.
Ya Allah! Ka sa mu cika da kyau da Imani. Amin.