TAMBAYA: Wanene Zulkarnaini, sannan a wani kasa ya rayu, kuma shin Annabin Allah ne ko ko a’a?
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.
Zulkarnaini ya kasance Sarki ne adali a bayan kasa, kuma Salihin bawan Allah ne Musulmi, Ya yi mulkin duk duniya kuma yakarade duniya gabas da yamma yana yada Tauhid da Musulunci, yayi raga-raga da kafirci da zalunci a bayan kasa. Kuma sarki zulkarnaini yayi zamani ne tare da Annabi Ibrahim Alaihis Salam. A cikin zance mafi inganci.
Malaman tarihi sun ruwaito ra’ayoyi mabambanta akan Zulkarnaini, An ce sarki ne na Daular farisa, an ce Annabi ne, wasu ma sun ce mala’ika ne shi zulkarnainin. An ce yayi rayuwa ne a kasar Himyar zamanin Annabi Musa ko Zamanin Annabi Ibrahim. Sannan an ce katangar da ya gina tana kasar Sin ne wasu suka ce tana cikin Taikun Atalantic wasu kuma sun ce ba’a san inda take ba. An samu sabani mai yawa a cikin tarihin wannan bawan Allah.
Allah Ta’ala ya ambaci Kissar zilkarnaini a al-Kur’ani Mai Girma cikin suratul Kahfi (sura ta 18 aya ta 83 – 98) Allah ya yabe shi da adalci, da girman mulkin da yahade gabas da yamma. Kuma shi ne ya gina katangar da ta tsare Yajuju-da-Majuju daga barna a cikin duniya.
Kissar Zulkarnaini tana daga cikin tambayoyi Uku da Yahudawa suka sa Mushirikan Larabawa suyiwa Ammabi Muhammad SAW tambaya a kai. Lalle kissa ce da ke cike da labarai mabambanta. Kissar na cikin littafan Yahudu da Nasara. Saidai a matsayin mu na musulumai, za mu iya karanta duk labaran kuma mu saitasu da abinda al-Kur’ani ya kissanta mana.
Lalle a kwai abin al’ajabi da lura da kuma darussa da dama da zamu fa’idantu da su a Najeriyar mu a yau, a cikin tarihin Zulkarnaini:
1. Mulki, mukami, shugabanci, daraja da daukaka duk na Allah ne, kuma yana badawa ga wanda ya so, a lokacin da ya so kuma yadda ya so.
2. Duk mai wata daukaka na shugabanci, toh kada yayi girman kai, da nuna Izzah da isa, ko yayi tunanin yafi kowa.
3. Aldalci shi ne ginshikin kasaitaccen mulki wanda duniya za tayi alfahari da shi ko bayan tafiyar mai mulkin.
4. Mulki da shugabanci ana amfani da shi ne don inganta rayuwar al’umma ba don tara abin duniya ba.
Allah shi ne mafi sani.
Discussion about this post