TAMBAYA: Shin ladar Sallar namiji a Jam’i daidai yake da na mace a gida?

0

TAMBAYA: Salamun Alaikum Mallam. Ance Sallar Maza a cikin jam’i yanada daraja 27. Mata da suka yi a gida, su ma hakane ? Kadan hakane, akwai hadisin da ya tabbatar da haka game da mata?

AMSA: Wa Alaikumus Salamu ya ‘yan uwa masu girma. Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Lalle Hadisai da yawa sun nuna falalar sallar mata a cikin dakunan su, fiye da yin jam’i a masallaci. Amma kuma musulunci bai hanasu yin jama’i ba, a masallaci ne ko a gida, mata nada damar yin jam’i karkashin liman( namiji).

Hadisi ya inganta cewa Sallar maza a cikin jam’i nada daraja 27 a lokacin da a ke karatu a bayyane, kuma tanada daraja 25 a Sallar asirce. Sai dai maza kadai ne aka umurta da zuwa jam’i, a yayinda mata a kace tasu Sallar a daki tafi daraja. Nana Ummu-Salama ta ruwaito Hadisi daga Annabi SAW yana cewa: Mafi alkhairin masallacin mata qurayar dakinsu. (Imamu Ahmad 6/297). Akwai wata mata a cikin sahabbai da tace ya Rasulallah! Ina kwadayin binka Sallah, sai Annabi SAW yace: hakika kisan cewa Sallah a dakinki tafi daraja.

Duk da cewar wasu malamai anaba mata daraja 25-27 idan sunje masallaci, tare da kuma cewa ni bansan wani hadisi dake ke cewa sunada daraja 25-27 idan sunyi sallar a gida ba, saidai a fahimtata, suma mata za su iya samun daraja 25-27 idan sunyi Sallarsu a cikin dakinsu.

Domin su an’umurce su ne da suyi Sallah a gida kamar yadda aka umurci maza da suyi a masallaci. Allah yana cewa: duk wanda ya aikata aiki nakwarai daga namiji ko mace … hakika zamu saka musu da lada mafi kyawon abinda suka aikata. |(suratun Nahl:97)

Allahu A’lamu

Share.

game da Author