TAMBAYA: Ina rokon malam ya fadi mani wani addu’a da zai rage mini damuwa da yake damuna
AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi
Muhammad SAW.
Ya Allah muna rokon ka da sunayen ka kyawawa ka yaye mana duk abinda ke damun baki daya.
Duk musulmin da ke cikin damuwa da kunci toh, ya yawaita Sadaqa ga mabukata, sadaqa da zata gusar musu da dauwar su.
Ba sadaqar Kuli-kuli, ko waina ko kusai.
Wato sadaqar da zata gusar da bukatar
mabukaci. Hadisi ya inganta daga Annabi SAW yace duk wanda ya magance matsar musulmi to, Allah zai magance matsalar duniya da lahira.
Abu na biyu shi ne bawa ya kyauta alakar sa da Allah ya bi umurninsa kuma ya tsare dokokin sa tare da tsare mu’amalar sa da sauran mutane.
idan bawa ya yawaita yin waddannan addu’o’i tah, zai samu saukin damuwar sa da yardan Allah:
1) Annabi SAW ya ce: Addu’ar Annabi Yunusa (AS) babu wani Musulmi da
zai roki Allah da ita, fa ce Allah ya biya bukatarsa. Addu’ar it ace:
LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZ-ZALIMINA.
لَا إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ سُبْحَانَكَ إِنِّي كُنْتُ مِنَ الظَّالِمِينَ
2) Annabi SAW ya ce: Addu’a da sunan Allah mafi girma karbabbiya ce:
ALLAHUMA INNI AS’ALUKA BI ANNA LAKAL HAMDU, LA ILAHA ILLA ANTA WAHDAKA
LA SHARIKA LAKA, ALMANNANU, YA BADI’AS SAMAWATI WAL ARDI, YA ZALJALALI
WAL IKRAMI, YA HAYYU YA KAYYUMU, INNI AS’ALUKAL JANNATA, WA A’UZU BIKA
MINNANNARI.
اللهمَّ إني أسالُك بأنَّ لك الحمدُ، لا إله إلَّا أنتَ وحدَك لا شريكَ
لك، المنّانُ، يا بديعَ السماواتِ والأرضِ، يا ذا الجلالِ والإكرامِ، يا
حيُّ يا قيومُ، إني أسالكَ الجنة، وأعوذُ بك من النارِ
3) LA ILAHA ILLAH KABLA KULLA SHAI’IN, WA LA ILAHA ILLAH BA’ADA KULLA
SHAI’IN, WA LA ILAHA ILLAH YABQA RABUNA WA YAFNA KULLA SHAI’IN.
لا إله إلا الله قبل كل شيء, و لا إله إلا الله بعد كل شيء , ولا إله إلا
الله يبقى رببنا ويفنى كل شيء .
4) LA ILAHA ILLAHAL AZIMAL HALIMA, LA ILAHA ILLAHA RABBIS SAMAWATI WAL
ARDA, RABBUL ARSHIL AZIMA, ALLAHUMMA INNI A’UZU BIKA MINAL HAMMI WAL
HAZNI WAL AJAZI WAL KASAL WAL BUKHULI WAL JUBNI WA GALABATIT DAINI WA
QAHRIL RIJAL.
لا إله إلا الله العظيم الحليم، لا إله إلا الله ربّ السّموات والأرض،
وربّ العرش العظيم، اللهم إنّي أعوذ بك من الهمّ والحزن، والعجز والكسل،
والبخل والجبن، وغلبة الدّين،قهر الرّجال.
ALLAH YA TSARARE MANA IMANINMU DA MUTUNCIN MU.
Tare da Imam Muhammad Bello Mai-Iyali.