Shugaban ‘Yan Sanda ya bada umarnin gaggauta janye jami’an sa da ke gadin manyan kasar nan

0

Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya bada umarnin a gaggauta janye ‘yan sanda masu gadi a gidaje da tsaron manyan kasar nan da kamfanoni.

Wannan doka ta zo ne a daidai domin shugabannin ‘yan sanda na baya kafin Idris, sun sha kafa dokar amma sai a shiriritar da ita, tun kafin a janye su.

A wani taron gaggawa da ya yi da kwamishinonin jiha da AIG na shiyyoyi yau a hedikwatar rundunar a Abuja, Idris ya ce dukkanin su su gaggauta daukar wannan umarni da gaggawa su aiwatar da shi.

Dokar ta ce a janye jami’an yan sanda masu gadin wasu manya da kamfanoni, amma banda cibiyoyin hada-hadar kudade, kamar bankuna da sauran su, a dukkan fadin kasar nan.

Haka Mataimakin Kwamishina Yomi Sogunle ya bayyana bayan kammala taro. Sogunle shi ne shugaban bangaren karbar koke-koke.

Ya kuma ce an janye duk wata lambar mota ta musamman wadda ba iri daya ta ke da sauran lambobi ba. Don haka duk mai irin ta to sai ya sake wata. Haka ya shaida wa PREMIUM TIMES.

Wannan gargadi shi ne na farko a cikin shekara goma. Duk sauran na baya da shi, ko sun yi kokarin hanawa, abin shiriricewa ya ke yi.

Share.

game da Author