A wani abin al’ajabi da tashin hankali da ya auku a garin Kaduna da safiyar Asabar, mutane sun uni suna tofa albarkacin bakin su game da yadda shugaban jam’iyyar APC bangaren Sanata Suleiman Hunkuyi Danladi Wada ya bace bat daga zuwa sallar Asuba.
Kamar yadda babban dan Wada Abdulmumini Wada ya shaida wa PREMIUM TIMES ya ce mahaifin su ya fita sallar Asuba ne da wajen karfe biyar da rabi amma har yanzu bai dawo gida ba sannan basu san inda yake ba.
” Gashi babu yadda za a iya neman sa ta waya domin duk wayoyin sa na gida. Yanzu dai muna zaton masu garkuwa ne suka arce da shi.
Bayanai sun nuna cewa hatta jami’an tsaro da aka tuntuba ko yana tare da su ne, sun ce basu da masaniyar inda Danladi ya ke zuwa yanzu.