SHEHU SANI YA FASA KWAN: Bayan albashin naira 750,000, ko wani Sanata na karbar miliyan 13.5 duk wata

0

Duk da boye-boyen da sanatoci suke tayi wa mazabun su na kin fadin abinda ake biyan su a majalisa duk wata, gashi a arha Sanata mai wakilan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani ya fasa kwan.

Shehu Sani ya bayyana cewa ko shakka babu kowani Sanata da ke majalisar dattijai a Najeriya na karbar naira miliyan 13.5 duk wata domin gudanar da ayyukan ofishin sa, bayan naira 750,000 ya ke karba a matsayin albashin sa.

Bayan haka kuma ya ce kowani Sanata na da naira miliyan 200 a ajiye domin yi wa mazabar sa ayyuka.

” Za a gaya maka cewa akwai wasu kudade ajiye domin ayyukan mazabar ka. Kai ne zaka je ka fadi musu abinda za kayi wa mutanen ka, daga nan sai ma’aikatan da ke rike da kudin ta yi maka aikin. Sai dai abin akwai kamu-kamu a cikin sa.

” Inda ko Kamu-kamun ya ke shine akan iya cinye kudin kuma ba ayi aikin ba.

” Abin da yanzu zai yi ma hakan wuya shine akwai kungiyoyi masu zaman kanzu da ke duba yadda ake kashe wadannan kudade na ayyukan mazabun.

” Idan don ta nine, a daina ba dan majalisa kudi irin wannan, a barmu da albashi kawai yafi. Ka ga za a fi maida hankali wajen yin ayyukan da ya kai mutum majalisa ba tunanin yadda za ka gina rijiyoyi ba ko kwalbati da dai sauran su a mazabun na.

Wannan dai shine karo na farko da wani dan majalisa zai fito ya fadi abinda ake biyan su.

Share.

game da Author