A yau Talata ne wani shugaba a cocin ‘Celestial Church’ dake Bayan Dutse, Narayi karamr hukumar Chikun jihar Kaduna Dele Ara ya bayyana yadda wani matashi a cocin su mai suna Sylvester Friday dan shekar 21 ya rasu.
Ya ce Friday wanda ke aikin gini da wannan coci ya rasu ne sanadiyyar fadawa cikin rafin dake kusa da wurin da yake aikin da limamin cocin Steven Shittu ya sa shi yi.
” Limamin cocin ya kula cewa rairayin kasa na kokarin cinye wani bangaren filin cocin wanda hakan ya sa ya kira Friday domin ya gyara wurin.”
” Yayin da yake aikin ne sai ya fada wani rafin dake kusa da wannan wuri amma limamin cocin da wannan coci ba sa aikata tsafi.
Idan ba a manta ba a ranar Alhamis din da ta gabata ne PREMIUM TIMES ta rawaito yadda wasu matasan unguwan suka kona cocin da ofishin ‘yan sanda kurmus sanadiyyar mutuwan wannan matashi.
Bayanai sun nuna cewa matasan sun kona cocin ne saboda suna zargin limamin cocin da kashe wannan matashi dan uwan su.
Matasan sun zargi limamin cocin mai suna Steven Shittu da yin amfani da shi wannan dan uwa nasu wajen yin asiri, wato tsafi.
Discussion about this post