Rundunar ‘yan sanda ta karyata rahotanin kai hari a wasu kauyukan jihar Kogi

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kogi ta karyata rade-radin da mazauna kauyukan Agbenema, Aj’Ichekpa, Opada da Iyade dake karamar hukumar Omala suka yi ta yadawa wai an kai musu hari har sarki Musa Edibo da matar sa sun rasa rayukan su a rikicin.

Gidan jaridar ‘PunchNewspapers’ ta rawaito cewa wasu maikiyaya ne suka kai wa wadannan kauyuka hari inda suka kona gidaje da sanadiyyar haka.

‘‘Wadannan makiyaya sun boye ne a cikin dajin dake kusa da wadannan kauyuka inda sai da suka sami sararin kai hari sannan suka far musu.”

Amma ko da PREMIUM TIMES ta tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar Ali Janga game da wannan hari, Ali ya ce babu kanshin gaskiya game da wannan hari da aka ce an kai wadannan kauyuka.

” Bani da masaniya kan harin da aka yi sannan babu gaskiya a cikin wannan batu domin babu inda aka kai wa hari a fadin jihar Kogi.” Ya ce.

Bayan haka ita ma sakatariyar yada labaran gwamnan jihar Petra Onyegbule ta karyata faruwan wannan al’amari.

Share.

game da Author