Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi ta sanar cewa mutane uku sun rasu a rikicin da aka yi tsakanin makiyaya da manoma a kauyen Igbeagu dake karamar hukumar Izzi a jihar.
Kakakin rundunar Loveth Odah ce ta sanar da haka ranar Litini inda ta bayyana cewa rikicin ya faro ne da safiyar wannan rana a daidai wani mazaunin kauyen ya gamu da wasu makiyaya Fulani biyu a daji yayin da ya je ciyar da awakin sa.
” Haduwar su ke da wuya sai fada ya kaure inda wadannan makiyaya biyu suka sare hannun shi mazaunin kauyen. Daga nan ne fa ya kantara ihu, yana neman dauki. Nan da nan kuwa sai wasu ‘yan uwan sa suka kawo masa taimako. Daga nan kuwa sai abu ya lalace inda suka ji wa juna ciwo su kuma makiyayan suka ruga cikin daji.”
Odah ta ce mazaunan kauyen sun kamo wadannan makiyaya kafin su fice daga kauyen suka lakada musu dukan tsiya sannan suka mika su ga sojojin dake sintiri a kauyen.
Ta kuma ce cikin wadanda makiyayan suka sara biyu sun rasa rayukan su a asibiti sannan daya cikin makiyayan ya rasu sanadiyyar dukan da ya sha.
Daga karshe Odah ta yi kira ga mutanen kauyen da su hanzarta kai kara ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa da su a duk lokacin da wani rikici irin haka ya kunno kai, sannan su guji daukan doka a hannun su.
Discussion about this post