Rikici ya sake barke wa a kauyen Filato

0

A ci gaba da samun rashin zaman lafiya da akeyi a wasu kauyukan jihar Filato, a safiyar Laraba din nan wasu mahara sun far wa kauyen Dong, inda rahotannin da ya iske mu suka nuna cewa an kona wasu gidaje sannan wasu motocin hawa ma dake ajiye a kauyen basu sha ba.

” A yanzu haka da nake magana da ku ina jin harbin bindiga daga nesa da gida na. Mun yi ta kiran jami’an tsaro su kawo mana dauki amma inaa. ” Inji wani mazaunin kauyen Dong da ya tattauna da PREMIUM TIMES ta wayar tarho.

Kakakin rundunar ‘Yan sandan jihar Filato ya sanar cewa lallai sun sami labarin wannan hari, kuma su aika da jami’an ‘yan sanda na rundunar Rantiya domin kwantar da tarzomar.

Bayan haka kuma gwamnan jihar Simon Lalong ya kori shugaban riko na karamar hukumar Bokoss, Simon Angol saboda gazawar sa na tsayar da tashin tashina da ake ta yawan samu a kauyukan karamar hukumar na Bokoss.

Share.

game da Author