RIGAKAFI: Bill Gates, Dangote da gwamnonin arewa shida sun saka hannu a takardar yarjejeniyya

0

Shugaban gidauniyyar Bill da Melinda Gates, Bill Gates, shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote tare da gwamnonin arewa shida sun saka hannu a takardar yarjejeniya domin inganta samar da alluran rigakafi a jihohin su.

Bill Gates wanda ya sanar da haka ya bayyana cewa gwamnonin sun yi haka ne domin su sami damar yi wa adadin yawan yaran suka bukaci allurar rigakafin a jihohin su.

Gwamnonin sun ce dalilin saka hannu a wannan yarjejeniya za su sami damar yi wa yara kashi 80 bida 100 allurar rigakafi a 2019.

Gwamnoni shida da suka sa hannu a wannan yarjejeniyar sun hada da Aminu Tambuwal, jihar Sokoto, Kashim Shettima jihar Borno, Abdullahi Ganduje, jihar Kano, Muhammed Abubakar, jihar Bauchi, Nasir El-Rufai, jihar Kaduna State da Ibrahim Geidam gwamnar jihar Yobe.

Share.

game da Author