Riciki ya kaure tsakanin jami’an Soji da ‘Yan sanda da na hukumar FRSC a Abuja

0

A safiyar Laraba din nan ne rikici ya kaure tsakinin jami’an Soji da ‘Yan sanda da na hukumar FRSC a unguwar Zone 7 dake Abuja.

Jami’an sun gwabza ne a daidai sun zo mika takardar gargadi tare da hukumar AEBP a ofishin hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC inda hakan bai yi wa jami’an hukumar FRSC dadi ba. Ana haka ne su jami’an Soji da na’yan sandan da suka zo wurin tare da AEBP suka far wa wata jami’an FRSC.

A haka dai dukkan su sun kama wasu daga cikin ma’aikatan juna inda suka ce baza su sake su ba. Kowa na fadin cewa sai daya ya saki wanda ya ke rike da shi kafin shima ya sake wanda ke hannun sa.

Har yan yanzu dai ana nan ana ta cacan baki tsakanin su.

Share.

game da Author