Ya zuwa ranar Alhamis ta 1 Ga Maris, 2018, an cika kwanaki 52 cur a jere ba kakkautawa, mabiyar Sheikh Ibrahim El-zakzaky wato Shi’a su na jerin-gwanon zanga-zangar lumanar a saki malamin na su.
Ana tsare da shi ne tun bayan farmakin da sojoji suka kai gidan sa cikin watan Disamba, 2015, inda aka ji masa ciwo shi da uwargidan sa Zeenat.
An dai kashe daruruwan mabiyan sa a farmakin kwanaki biyu da sojoji suka yi musu a Zari’a. Duk da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta bayyana cewa a saki malamin tun cikin Disamba, 2016, har ta bayar da umarnin a cikin kwanaki 45 za a gaggauta sakin nasa da uwargidan sa, har yau gwamnatin tarayya ta ki sakin sa, a dalili na tsaro.
DANDALIN ABUJA UNITY FOUNTAIN
Tun da mabiyan sa su ka fara zanga-zanga a Abuja, sai suka samu goyon bayan wasu kungiyoyin kishin jama’a, inda irin su Deji Adeyanju suka narke cikin masu muzaharar a saki Zakzaky.
Sun maida Dandalin Unity Fountain wurin zaman-dirshan su na jimamin tsare malamin tare da yin jawabai da raba kasidu.
Unity Fountain dai nan ne dabdalar ’yan #BringBackOurGirls. Su ma masu neman a saki Zakzaky, suna taruwa a wurin a kullum su na yin zaman-dirshan tare da sauran kungiyoyin kare hakkin dan Adam da ba su da alaka da addini, amma su na tausaya wa Sheikh Zakzaky.
Baya ga zaman-dirshan da su ke shi a kullum, a kowane yammaci kuma su kan yi zanga-zangar lumana su na bin titinan Abuja su na kabbarori, wakoki, fareti, zanzan, dukan kirji da tsallen yi wa kwalta dirar rashin tausayi.
Daga cikin wakokin da suke yi, akwai, “No surrender har abada, a saki El-zakzaky.” Akwai kuma, “mu ne masu kunnen kashi, tilas sai an saki El-zakzaky.”
Tun su na yi ba su da yawa sosai, har suka kai daruruwa, yanzu har sun sun kai dubbai, kuma mazan su da matan su. Manya da matasa.
Idan su ka tada cidar zanga-zanga daga Unity Fountain su ka darkaki wata unguwa, gobe kuma sai su dauka daga wata unguwa su karada cikin Abuja.
MUZAHARA A MASALLAN JUMA’A
Yau su ne a Central Area, gobe a Kasuwar Wuse, jibi kuma a Tashar Motar Jabi. Wata rana su dauka daga Banex Plaza wata rana kuma daga Area 1 ko Area Eleven. Ga su nan dai ko a Babbar Gadar Berger ko a fankacecen shataletale da ya fi kowane fadi a Najeriya, wato randabawul na Life Camp.
Banda zanga-zanga, wacce su ka fi kira muzahara, a kowace Juma’a kuma sukan yi dandazo a wani masallacin Juma’a daya tal alahirin su, babu wanda zai yi zaton su na wurin, sai dai bayan an kammala sallah ka rika jin kabbarori na tashi kamar wurin zai fashe.
Sun sha yi a Babban Masallacin Abuja, sun yi a na Area 1, wanda aka fi sani da Masallacin Shagari, sun yi a Masallacin Zone 3 kusa da hedikwatar Hukumar Kwastan ta Kasa da sauran masallatan Juma’ar da ke cikin Abuja.
Tun jami’an ‘yan sanda na artabu da su, har sun daina, ko kuma sun hakura, ko kuma sun fahimci kyale sun shi ya fi sauki.
Irin yadda su ke fitowa bakin-rai-bakin-fama, sai dai a kashe su, mai yiwuwa shi ke sa jami’an tsaro yin baya-baya ko shan jinin jikin su, kada a bude wuta a sake yin mummunar barna kamar wadda aka yi a Zariya cikin 2015.
YANAYIN MASU MUZAHARA
Tun da suka fara tsawon kwanaki 52 a jere, ba mai dauke da sanda, gora, wuka, adda, takobi ko bindiga. Kowane hannu biyu yake, amma da gani ka san sun muka rayuwar su, sun sallama, ko su koma gida, ko ba su koma ba. Su na dai dauke da manya da kananan fastoci masu rubutun a saki Zakzaky, ko da Hausa ko kuma da Turanci.
Sai dai hakan bai hana gwabzawa da jami’an ‘yan sanda a karon farkon muzaharar ba. Wani harbi da suka yi zargin ‘yan sanda sun yi musu, ya yi sanadiyar kisan mutane uku da jikkata da dama.
Daga cikin wadanda suka rasa ran su, har da wakilin Sheikh Zakzaky na Sokoto, Malam Qassim, wanda aka harba, bayan kwanaki biyar ya rasu a wurin jiyya a wani a Kano.
Ko da ya ke ‘yan sanda sun jajirce cewa a lokacin ba su yi harbi ba, sun dai harba barkonon tsohuwa kawai.
Muzaharar da su ka ta fara jan hankalin jama’a zuwa gare su. Yayin da wasu ke gann cewa kamata ya yi a sakar musu jagoran su domin Abuja ta daina ganin ana wannan zanga-zanga, wasu kuma sun fara jajanta musu, musamman ganin cewa ba su dauke da makamai.
Akasarin masu muzaharar ba a cikin Abuja suke kwana ba. A kullum su na shigowa gari ne daga garuruwa irin su Suleja, Zuba, Maraba, Nyanya da sauran su. Kuma dama sun je ne daga garuruwa da kyauyuka masu nisa na Arewacin kasar nan.
ASUSUN TAIMAKEKENIYA
Saboda matsalar rashin wadatar kudin motar shiga Abuja da cin abinci, sai suka kafa wani asusu, inda suka rika tura sakon neman taimako ta soshiyal midiya, amma daga wurin mabiya wadanda ba za su samu damar zuwa ba.
Suna asusun “ka wakilce mu a aljihun ka, mu wakilce ka a Abuja.” Wato wanda ba shi da halin zuwa, to ga lambar asusun banki nan da za ka rika zuba naira 100 kacal a kullum, ko kuma ranar da ka ke da hali.
Da wadannan kudaden da suke tattarawa ne ake sallamar marasa karfi su samu kudin mota. Kuma akan sayi ruwan sha da dan abin da ya saukaka a Unity Fountain idan ana zaman dirshan.
A iyar kwanakin da PREMIUM TIMES Hausa ta rika bin diddigin sanarwar kudaden da ake tarawa a kullum, ta fahinci cewa a kullum ana bayyana abin da aka samu a bainar jama’a a Unity Fountain.
PREMIUM TIMES HAUSA ta tambayi wani dan jarida mai zaman kan sa, wanda ke a sanun gaban yada manufofin Sheikh Zakzaky a soshiyal midiya mai suna Bala Makosa. Ya bayyana cewa ai tabbas sun samu nasara a wadannan kwanaki da su ka yi su na muzahara.
“Ka da dai nasara ta farko, mun tilasta gwamanati ta fito mana da Malam, kowa ya san halin da ya ke ciki. Ka san kuwa da ba mu shigo Abuja ba, ba za su taba fito da shi har a gan shi ba.
“Nasara ta biyu kuma ita ce, gwamnati ba yadda za ta yi da mu, ba ta dai son mu na wannan muazahara a Abuja, saboda mutuncin ta na zubewa a idon dofilomasiyyar duniya. To mu kuma ba makamai mu ke dauke ba. Babu ruwan mu da makamai, tunda mu ba ‘yan ta’adda ba ne. Abin da kawai mu ke cewa a saki Sheikh Zakzaky kawai, shikenan.”
ARTABU DA ’YAN SANDA
A can baya an sha watsa musu ruwan zafi, amma sun dake, an sha watsa musu barkonon tsohuwa, sun dake, kai har artabu an yi da su a daidai kofar shiga tashar Jabi, tsallake ofishin jaridar Thisday da ke Abuja, a lokacin da ‘yan sanda suka kama wasu masu zanga-zanga uku, amma suka bi suka kwato ‘yan’uwan su.
Da yawan wadanda PREMIUM TIMES HAUSA ta yi hira da su, sun bayyana cewa su na nan daram a Abuja, ba ranar komawa gida, sai an saki jagoran su El-Zakzaky da uwargidan sa, Zeenat.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa wasu daga cikin su kan koma gida su yi wanaki uku ko biyar su sake shirin komawa Abuja.
A duk lokacin da suke muzahara, jami’an ‘yan sanda kan rika bin su a baya ko a jefe, domin gudun wuce-gona-iri. Duk da dai har yau ba a wuce ba, hakan bai hana su yin ‘yar tirja-tirja da jami’an tsaro a wasu lokutan ba.
Da yawan wadanda PREMIUM HAUSA ta yi hira da su, sun nuna cewa zantsar zalunci ne a ci gaba da tsare jagoran na su, musamman tunda kotu ta ce a sake shi, ga shi an lahanta shi, an lahanta matar sa, kuma an kashe masa ‘ya’yan sa har guda shida.
Wata da PREMIUM TIMES HAUSA ta yi hira da ita, ta ce ai sun samu gagarimar nasara. “Domin ka ga ai a da ba mu ma taba zuwa Abuja yin muzahara ba. Amma yanzu ga mu muna muzahara kusa da Fadar Shugaban Kasa, kusa da Majalisar Tarayya, a Dandalin Eagle Square da dukkan wuraren da mu ke yi a cikin Abuja.”
To shin mabiya Zakzaky sun yi sabuwar Hussainiyya kenan a Abuja, tun bayan rushe musu ta Zariya da jami’an sojoji su ka yi?
GWAMNATI DA JAMI’AN TSARO NA KAN BAKAN SU
Jami’an tsaro da gwamnatin Najeriya har yanzu basu daga wa masu yin zanga-zangar kafa ba. A kullum suna nuna musu cewa abin da suke yi ba daidai bane. A haka gwamnati ta fitar da bayanai da dama tun bayan arangamar da sojoji suka yi da ‘yan kungiyar a Zariya cewa ba daidai bane bayanan cewa wai sun far musu ne kawai batare da sun ki bin dokar kasa ba.
Bayanan rahotannin da aka fitar, wanda gwamnatin Kaduna ta kafa, sun nuna cewa akwai rashin bin dokar kasa da kungiyar ba ta yi sannan suna yi wa gwamnati kage ne kan wasu abubuwan da suke fadi wai an aikata musu. Bayan haka an gano suna muzguna wa mutanen da suke makwabtaka dasu musamman a garin Zariya in da nan ne Hedikwatar kungiyar.
A wasu lokutta da dama gwamnati da jami’an tsaro kan koka kan yadda masu zanga-zangar ke far musu ko da bayan sun yi musu iya ka da inda zasu ya tattaki.
Duka da wadannan korafe-Korafe gwamnati da jami’an tsaro sun ja daga, su kuma yan kungiyar suna nan akan bakar su na sai fa an sako musu shugaba.
Discussion about this post